Sarkin Musulmi Ya Fallasa Babbar Matsala da Ke Kara Rura Wutar Hare-Haren ’Yan Bindiga a Arewa
- Mai martaba sarkin Musulmi ya nuna damuwarsa kan yadda kullum 'yan ta'adda ke yin wasa da hankalin jami'an tsaro wajen kai hare-hare
- Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce jami'an tsaro da gwamnati ba sa iya samun bayanan sirri har sai 'yan bindiga sun gama cin karensu ba babbaka
- Sarkin Musulman ya bayyana hakan ne a Bauchi, yayin da ya ke martani kan kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi wa mutane a jihar Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Bauchi - Mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya diga ayar tambaya kan fikirar jami'an tsaron Najeriya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa jihohin kasar.
Ya ce 'yan bindiga da masu aikata laifi kullum na shammatar jami'an tsaro yayin kai farmaki, wanda nakasu ne ga fikirar tattara bayanan jami'an.
Yan bindiga sun fi jami'an tsaro samun bayanan sirri - Sarkin Musulmi
Mai girma sarkin Musulman ya yi wannan maganar ne ranar Laraba a Bauchi, yayin gudanar da taron bitar da'awar Islama na kasa karo na 80, inda ya yi Allah wadai da harin Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi kira ga jami'an tsaro da su zamo masu kara kaimi wajen ayyukan leken asiri a kasar don samun bayanan sirri da zasu rinka dakile hare-haren 'yan bindiga, rahoton Channels TV.
Alhaji Abubakar III ya ce:
"Kullum ba mu da aiki sai yin Allah wadai, kuma ihu ne bayan hari, daga nan me muke tsinanawa? Da farko Tudun Biri, yanzu kuma Filato, shin ina gwamnati mai kare al'umma?"
"Me ya sa jami'an tsaro ba za su rinka samun bayanan sirri don kare faruwar hare-haren ba? Me ya samu fannin fikirar jami'an kasar nan? Kuna nufin ba wanda ke da masaniya kan hare-haren nan?"
Hare-haren 'yan bindiga matsalar shugaban ne ba addini ba - Sarkin Musulmi
Ya ce ko a jihohi irin su Sokoto, Kebbi da Kaduna, an gaza samun hanyoyin tattara bayanan sirri kan 'yan ta'adda, inda ya yi ce "yan bindiga kullum na gaba da mu wajen tunani".
Da ya ke martani kan yadda aka siyasantar da tsaro a Najeriya, sarkin Musulmai ya ce rashin shugabanci ne ke jawo matsalar tsaro ba wai siyasa ba.
Ya ce:
"Ba addini ba ne wannan, Musulmi da Kirista na shiga mota daya, su je kasuwa daya kuma su sayi kaya iri daya, kawai dai matsalar shugabanni ce, dole mu fadi gaskiya."
A karshe mai girma Abubakar Sa'ad III ya ce yana fatan nan da 'yan watanni shugabanni za su yi abin da ya dace don kawo karshe hare-haren ta'addanci a kasar.
Yan bindiga sun kai hari jihar Plateau, sun kashe daruruwan mutane
A ranar Litinin, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wasu 'yan bindiga suka dira karamar hukumar Bakkos da ke jihar Plateau inda suka kashe daruruwan mutane.
Wannan kazamin harin ya tayar da hankulan jama'a, inda shugaban kasa, gwamnonin Najeriya, 'yan majalisun tarayya suka yi Allah wadai, tare da neman daukar mataki.
Asali: Legit.ng