Abin Farinciki: Gwamna Radda Ya Tabbatar da Daukar Malamai 7,325 Aikin Gwamnati a Katsina

Abin Farinciki: Gwamna Radda Ya Tabbatar da Daukar Malamai 7,325 Aikin Gwamnati a Katsina

  • Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da ba malamai 7,325 takardar kama aikin din-din-din a jihar, hakan na nufin sun zama ma'aikata masu fansho
  • Dikko Umaru Radda, gwamnan jihar ne ya mika masu takardun, inda kuma ya yi masu nasiha da su kasance masu gudanar da ayyukansu cikin jin tsoron Allah
  • Radda ya kuma sha alwashin bai wa malaman horo na musamman kamin su fara aiki a ranar 6 ga watan Janairu 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Gwamna Umar Dikko Radda, ya mika takardun kama aikin din-din-din ga sabbin malamai 7,325 da aka dauka aiki a gwamnatin jihar Katsina.

Gwamnan wanda ya taya malaman murna, ya bukaci su kasance masu yin aiki tukuru kasancewar koyarwa tamkar jahadi ne saboda Allah.

Kara karanta wannan

Rikicin Wike da Fubara ya dauki sabon salo yayin da atoni janar na Ribas ya yi murabus

Gwamnatin Katsina ta dauki sabbin malamai 7,325 aiki
Gwamna Radda ya mika takardun kama aikin gwamnati ga sabbin malamai 7,325 a jihar Katsina. Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Gwamna Radda ya yi wa sabbin malamai nasiha

Ya ce Allah ne ya ba su wannan aikin don yi wa al'umma hidima, don haka su kasance malamai masu aiki da tsoron Allah da kuma koyarwa bisa gaskiya, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Radda:

"Allah ne ya zabe ku, kar ku ci amanarsa. Ku yi abin da ya dace kuma kar ku ci amanar jihar ku, ba zamu iya yi maku hisabi ba, amma Allah na jiran kowa a madakata.

Gwamnan ya kara da cewa ma'aikatar ilimi na samun sauye-sauye a jihar, don haka akwai bukatar sabbin malaman su zage damtse don bunkasa harkar ilimin jihar.

Gwamna Radda ya kuma yi alkawarin horas da sabbin malamai kafin tura su wuraren da za su aiki, inda ake sa ran za su kama aiki a ranar 6 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya nada tsohon soja a matsayin shugaban hukumar Hisbah, ya fadi dalili

Yan sanda sun kashe fitaccen mai garkuwa da mutane a Katsina

A wani labarin na daban, rundunar 'yan sanda ta sanar da kashe wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, Nazifi Ibrahim, dan asalin kauyen Unguwar Tsamiya da ke Faskari a jihar Katsina.

Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan sandan sun kuma yi nasarar kwato tarin alburusai na bindigu daban daban a sumamen da suka kai mabuyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel