Mafi Munin Sata da Rashin Gaskiyar da Aka Yi a Lokacin Mulkin Buhari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A lokacin yakin neman zabena a 2014, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yaki da rashawa, amma tun bayan shigar Buhari ofis a 2015, batu kan yaki da rashawar da ya yi alkawari ya zama kamar almara.
Wata kungiya mai rajin kare hakkin bil-Adama da kuma yaki da rashawa, ta nemi kotun laifukan ta'addanci ta tuhumi Buhari da Emefiele kan "laifukan da suka shafi cutuwar jama'a".
Kungiyar ta zargi Buhari da Emefiele da kitsa rashawa da satar dukiyar gwamnati ta hanyar kwangilar boki, cushe a kasafi, karkatar da kudaden ayyuka da sauransu.
Ga wasu manyan sata da rashin gaskiya da aka yi a zamanin gwamnatin Buhari kamar yadda Premium Politics ta wallafa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Badakalar Godwin Emefiele da sake fasalin naira
Sunan Godwin Emefiele ya yi shuhura tun bayan da ya canja fasalin Naira a zamanin Buhari, lamarin da ya haddasa karancin takardun kudi da tsadar rayuwa.
Wani mai bincike kan badakalar CBN da wasu bankuna, Jim Obaze, ya zargi Emefiele da boye biliyoyin naira a asusun bankuna 593 a Amurka, Burtaniya da China.
Ban da wannan ana kuma tuhumar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya da mallakar bankin Union, Sky da wani bankin ba bisa ka'ida ba.
Ana ganin duk abinda Emefiele ya kitsa da sa hannun Buhari tun bayan da ya ba shi damar fita kasar waje da sunan karo karatu, inda aka yi zargin ya yi hakan don ba shi damar tserewa daga tuhuma.
Ana zargin ministar Buhari da satar N37bn
Hukumar yaki da rashawa EFCC ta kama wani dan kwangila mai suna James Okwete kan zargin hada baki don satar naira biliyan 37 karkashin ma'aikatar ayyukan jin kai, bisa ikon tsohuwar minista Sadiya Umar Farouk.
Hukumar EFCC ta ce dan kwangilar ya bayar da bayanai kan Umar-Farouk da tsaffin daraktocin ma'aikatar, kamar yadda hukumar ke tuhumar ministoci uku a zamanin Buhari.
Bincike ya nuna cewa an wawure naira biliyan 37.1 daga asusun gwamnati zuwa wasu asusun bankuna 38, wadanda ke da alaka da dan kwangilar Okwete.
'Nigeria Air' - Batu kan jirgin saman Najeriya
Ma'aikatar sufurin jiragen sama karkashin Hadi Sirika suka gabatar wa Buhari bukatar dawo da jirgin Najeriya don samar da ayyuka da bunkasa masana'antar, amma wasu basu yarda ba,
Bincike ya nuna cewa tsohon ministan sufurin ya tuntubi hukumar jiragen saman Ethiopia kwanaki kafin mika mulki, don kawo jirgin da zai zama mallakin 'Nigeria Air'.
Sai dai an yi zargin tsohon jirgine Ethiopia ta kawo kirar Boeing 73-860 wanda ya nuna shekararsa 11 yana aiki kuma har Malawi ta taba amfani da shi, sabanin kudin da aka ware masa da sunan sabo.
Majalisar tarayya ta zargi Hadi Sirika da kitsa wannan makircin don karkatar da kudin jama'a inda aka ce ya kara kudin mallakar jirgin daga naira tiriliyan 1.5 zuwa naira tiriliyan 3 ba tare da hujja ko kwakkwaran dalili ba.
Shirin ciyar da daliban makaranta abinci
Gwamnatin Buhari ta kawo shirin ciyar da dalibai abinci a shekarar 2016, sai dai shirin ya fuskanci zarge-zargen rashawa da karkatar da kudin gwamnati ba tare da an yi shi yadda ya kamata ba.
An yi zargin cewa duk wani abu da ya shafi shirin bai yi tasiri kan dalilin kirkirarsa ba, face ma gaza kare makudan kudaden da aka batar ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
Maciji, Biri da satar biliyoyin naira
A watan Fabreru 2018, hukumar JAMB ta zargi maciji ya sace naira miliyan 36 daga ofishinta da ke Makurdi, jihar Benue, bayan da aka zargi Ms Philomina da satar kudin.
A shekarar ne kungiyar sanatocin Arewa suka cire Sanata Abdullahi Adamu matsayin shugaban kungiyar saboda ikirarinsa na cewar biri ya sace naira biliyan 70.
Majalisar dattawa ta 7 ce ta ba kungiyar sanatocin naira miliyan 70, amma aka yi ikirarin birai sun farmaki gidan gonar wasu sanatoci suka sace kudin.
Ko a shekarar 2022 sai da hukumar inshorar Najeriya ta ce wai Gara ta cinye takardun naira biliyan 17.128 da aka ajiye a cikin ofishin hukumar, wanda ake bincike kansu.
Ministar Buhari ta yi wa EFCC martani kan zargin satar N37bn
A wani labarin, tsohuwar ministar ma'aikatar ayyukan jin kai a zamanin mulkin Buhari, Sadiya Umar-Farouk ta nesanta kanta daga zargin badakalar naira biliyan 37
Umar Farouk ta ce ita sam ba ta taba sanin wani dan kwangila Okwete ba, kuma bai taba yi mata aiki ba, don haka za ta dauki mataki.
Asali: Legit.ng