Yadda Yan Sanda Suka Cafke Daliba Mai Bayar da Bayanai Ga Yan Bindiga, Ta Tona Asiri
- Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta yi babban kamu na wani ƙasurgumin ɗan ta'adda da ya addabi al'ummar jihar
- Kamun ɗan ta'addan mai suna Umar Aliyu ya sanya an yi caraf da wata ɗaliba ƴar shekara 18 mai ba ƴan bindiga bayanai
- Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da kamun ya ƙara da cewa har da cewa bayan ɗalibar, an kuma cafke wasu masu ba ƴan bindigan bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wata ɗaliba ƴar shekara 18 da haihuwa ta Kwalejin Kiwon Lafiya ta jihar Neja da ke Kontagora, Zubaida Sanusi, na tsare a hannun ƴan sanda.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin Zubaida ne bisa yin aiki a matsayin mai ba da bayanai ga ƴan bindiga.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya bayyana cewa an kama ɗalibar ne biyo bayan kama wani ɗan bindiga mai suna Umar Aliyu, wanda aka fi sani da Babuga Datijo mai shekaru 37.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yayin bincike an gano lambar ɗaya daga cikin ƴan bindigan da ake nema ruwa a jallo, Shaibu Haruna a cikin wayar ɗalibar, inda aka ajiye lambar a matsayin ‘Kuɗin-banza’.
Ya ce ɗalibar ta amsa cewa wata mata mai suna Aisha Mohammed ce ta gabatar da ita ga Shaibu, inda ta ƙara da cewa Shaibu ya kan bata kuɗi domin yin lalata da ita, rahoton Theeagleeye ya tabbatar.
Ta wacce hanya aka gano ɗalibar?
Kwamishinan ƴan sandan ya ce ƙoƙarin da aka yi na cafke wasu ƴan kungiyar ta Aliyu, ya sa aka gano wata lambar waya a Kontagora mallakar ɗalibar da ake zargin.
Ya ce shugaban ƙungiyar ya bayar da lambobin wayar wasu ƴan ƙungiyar guda biyu Maidabo da Shaibu Haruna na garin Garatu, ƙaramar hukumar Bosso.
Ya ce an kama wani Motse Mohammed mai shekaru 47 da Aliya Mohammed mai shekaru 48, mazauna garin Salka, ƙaramar hukumar Magama da laifin tuntubar ƴan bindigar tare da zama masu ba da bayanai a wasu hare-hare.
Ya ce rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa ƴan bindigan sun aike da naira dubu 10 ga mutanen biyu ta hanyar wani POS a garin Salka.
Ƴan Bindiga Sun Halaka Direba a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun buɗe wuta kan wata motar jigilar fasinjohi a jihar Neja, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar direban motar.
Ƴna bindigan sun kuma yi awon gaba da dukkanin fasinjojin da ke cikin motar ziwa cikin daji.
Asali: Legit.ng