Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Yi Garkuwa da Shugaban APC a Jihar Arewa

Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Yi Garkuwa da Shugaban APC a Jihar Arewa

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon shugaban APC na ƙaramar hukumar Wushishi a jihar Neja
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun kai farmaki garin Zungeru ranar Alhamis da daddare, suka buɗe wuta kafin su tafi da ɗan siyasan
  • Hukumar yan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin amma mazauna garin sun ce yan bindigan sun jikkata mutum biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki cikin garin Zungeru da ke jihar Neja a yanakin Arewa ta Tsakiya ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023.

Yan bindiga sun sace shugaban APC a jihar Neja.
Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban APC a Jihar Niger Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro rahoton cewa yayin wannan harin ƴan bindigan sun yi garkuwa da tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Wushishi, Alhaji Sule Muhammad.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari a arewa, sun tafka ɓarna mai muni tare da kashe bayin Allah

Ƴan bindiga sun kutsa cikin garin da sanyin safiyar ranar Alhamis, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka yi awon gaba da ɗan siyasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda maharan suka jikkata mutum biyu

Wasu mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tafi da tsohon shugaban APC da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar daren ranar Alhamis.

A cewarsu, maharan sun kuma raunata ɗiyarsa da ɗansa a kokarin tafiya da mahaifinsu.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Lokacin da suka shigo garin ranar Alhamis, sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi kuma sun ɗauki kusan sa'a ɗaya kafin su tafi da tsohon shugaban APC na ƙaramar hukumar Wushishi, Alhaji Sule."
"Sun harbi ɗiyarsa a ƙafa kuma sun raunata ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza da wuƙa. Har yanzu da nake magana da ku ba su kira danginsa ba."

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Ɗaya daga cikin ɗalibai mata na jami'ar tarayya da yan bindiga suka sace ta kuɓuta

Yayin da aka tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ta wayar tarho bai ɗaga kiran da aka masa ba.

APC ta rushe shugabanninta na jihar Ribas

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta ƙasa ta kori dukkan shugabanninta na jihar Ribas ta naɗa sabon kwamitin rikon kwarya.

Jam'iyyar ta cimma wannan matsaya ne a wurin taron kwamitin gudanarwa NWC na ƙasa karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel