Akwai Haske a 2024: Tinubu Ya Yi Gagarumin Alkawari Gabannin Shiga Sabuwar Shekara, Ya Fadi Dalili

Akwai Haske a 2024: Tinubu Ya Yi Gagarumin Alkawari Gabannin Shiga Sabuwar Shekara, Ya Fadi Dalili

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da ba da tallafi saboda wahalar da ake sha a kasar
  • Tinubu ya nemi hadin kan ‘yan kasar ganin yadda ake shan wahala inda ya ce sabuwar shekara za ta zo da abin mamaki
  • Tinubu ya bayyana haka ne yayin sakon taya al’ummar Kiristoci bikin Kirsimeti a kasar inda ya nemi goyon bayan al’umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin kawo sauyi ga ‘yan Najeriya yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin sakon taya al’ummar Kiristoci bikin Kirsimeti a kasar inda ya nemi goyon bayan al’umma.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Tinubu ya yi alkawarin sauya wahalhalun da 'yan kasar ke sha da jin dadi a 2024
Tinubu Ya Yi Gagarumin Alkawari Samar da Sauki Yayin da Ake Shirin Shiga Sabuwar Shekara. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Getty Images

Wane alkawari Tinubu ya yi?

Shugaban ya ce tabbas akwai hasken nasara a shekarar da za ta kama nan da mako daya, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba ba shi goyon baya don tabbatar da himmatuwar gwamnatinsa kan jin dadinsu da walwala.

Wannan shi ne karon farko da shugaban ya yi bikin Kirsimeti a kan kujerar mulki inda ya bukaci ‘yan kasar su ci gaba da kishin kasa.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba kamar yadda take yi don ganin ta dakile irin wahalhalun da ake sha a kasar tare da farfado da tattalin arzikin kasar.

Wane roko Tinubu ya yi ga 'yan kasar?

Ya ce:

“Ga dukkan masu bi, wannan wata dama ce da zamu yi murna tare da taimakawa ‘yan uwa da abokan arziki.

Kara karanta wannan

Yadda Abba Gida-Gida ya samu matsala, aka yi laifi wajen Rusau a Jihar Kano

“Har ila yau, lokaci ne na taimakon juna ganin yadda shekarar ta zo da kalubale na wahalhalu ga ‘yan kasar.”

Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da tallafi saboda wahalar da mutane suka shiga, cewar Leadership.

Ya kuma bukaci ‘yan kasar su ci gaba da yi wa jami’an tsaro addu’a ganin yadda suka sadaukar da rayuwarsu don kare kasar.

Natasha ta yi rabon kaya a Kogi

A wani labarin, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi rabon kayayyaki yayin da ake tsaka da bikin Kirsimeti.

Natasha ta ce ta yi hakan ne don saukaka wa jama’ar mazabarta ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.