Binciken da Aka Yi a CBN Ya Bankado Abubuwan da Emefiele Ya Aikata a Lokacin Buhari
- Godwin Emefiele ya boye kudi masu yawa a bankunan kasashen waje a lokacin da yake gwamnan bankin CBN
- An gano wannan ne a sanadiyyar aikin da Kwamitin Jim Obaze ya yi, kuma ya mika rahoton ga shugaban kasa
- Ana zargin akwai dokokin da Emefiele ya saba wajen buga kudi, laifin zai iya shafan wasu manya a bankin CBN
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wani dogon rahoto ya nuna ana zargin Godwin Emefiele da boye biliyoyin Nairori a kasashen waje da yake rike da bankin CBN.
Punch ta ce ana zargin Godwin Emefiele da boye kudi a kasashen Amurka, Birtaniya da Sin ba tare da amincewar shugabannin CBN ba.
Kudin da Godwin Emefiele ya boye a waje
Wani bincike na musamman da Jim Obaze ya gudanar, ya nuna a Ingila kadai, tsohon gwamnan ya boye £543, 482,213 a bankuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin Jim Obaze ya kammala aikinsa, kuma ya gabatar da rahoto gaban Bola Tinubu wanda ya nuna an boye kudi cikin asusu 593.
Za a koma kotu da tsohon Gwamnan CBN, Emefiele?
Obaze ya bibiya ya gano duka bankunan da Godwin Emefiele ya yi wannan aiki, ana tunanin gwamnati za ta tuhume sa da karin laifuffuka.
Jaridar ta tuntubi lauyan tsohon gwamnan, Mathew Bukkaa, SAN, amma bai yi magana ba.
CBN: Za a iya taba na-kusa da Buhari
Watakila a gurfanar da tsohon gwamnan bankin a kotu bisa sabawa sashe na 19 na dokar CBN, shari’ar za ta iya shafar irinsu Tunde Sabiu.
Baya ga tsohon hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Leadership ta ce ana zargin akwai hannun manyan Darektoci 12 na babban bankin.
Emefiele da badakalar canjin kudi a CBN
Duk canjin kudin da aka yi a shekarar nan, an yi ne ba da asalin amincewar shugaban kasa ba, na kusa da shi aka yi amfani da su.
Kamfanin De La Rue da ke Ingila aka ba kwangilar buga sababbin kudi a kan N61.5bn, bincike ya nuna CBN ya biya kamfanin N31.79bn.
Binciken ya tono yadda aka yi amfani da bankin CBN wajen cin bashin da ya sabawa ka’ida wanda tsofaffin gwamnoni sun soki lamarin.
Sabon Gwamna ya shiga bankin CBN
Ana da labari Micheal Yemi Cardoso ya sha bam-bam da Godwin Emefiele, yadda za a gyara bankuna ne kurum a gaban shi ba bada tallafi ba.
Sabon gwamnan da aka nada a CBN babu ruwansa da harkokin da ba aikin babban banki ba irinsu harkar noma da kananan kasuwanci.
Asali: Legit.ng