Nazarin Shekarar 2023: Jerin Munanan Abubuwa 8 da Su Ka Faru Masu Tayar da Hankali a Najeriya

Nazarin Shekarar 2023: Jerin Munanan Abubuwa 8 da Su Ka Faru Masu Tayar da Hankali a Najeriya

Shekarar 2023 ta zo da wasu iftila’i da ke tattare da ita kamar yadda sauran shekaru su ke zuwa da su a Najeriya.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sannan akwai wasu abubuwa da su ka faru a shekarar wadanda ke dauke da dumbin darasi a kasar.

Jerin abubuwa 8 ma su tayar da hankali da su ka faru a 2023
Shekarar 2023: Jerin Munanan Abubuwa 8 da Su Ka Faru. Hoto: Giro Argungu, Abba Kabri Yusuf.
Asali: Facebook

A ko wace shekara ana samun irin wadannan abubuwa da ke faruwa a matsayin jarrabawa ga ‘yan kasa wanda ubangiji ke jarabtarsu.

Legit hausa ta jero muku manyan abubuwa marasa dadi da su ka faru a shekarar 2023:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Harin bam kan masu Maulidi a Kaduna

A ranar Lahadi 3 ga watan Disamba ce rundunar sojin kasa su ka saki bam kan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kano: Zanga-zanga ta sake barkewa a Kudancin Najeriya kan hukuncin jihar, sun nemi bukata mai girma

Akalla mutane fiye da 120 su ka mutu inda da dama su ka samu raunuka a Kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar.

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin yin bincike tare da daukar mataki kan lamarin da gaggawa, cewar Aljazeera.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce a kasar da ma kasashen ketare inda kowa ke yin Allah wadai da wannan hari na ganganci.

Har ila yau, kungiyoyi da dama sun yi Allah wadai da wannan harin inda su ka bukaci yin bincike mai tsauri.

2. Rasuwar Sheikh Giro Argungu

A ranar 6 ga watan Satumba ce da yammacin aka sanar da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu.

Shugaban Kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau shi ya sanar da rasuwar malamin inda ya tabbatar da cewa Giro ya rasu bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Manya-manyan malaman kasar baki daya sun halarci sallar jana’izar malamin tare da yi masa addu’ar samun rahama.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna

3. Rasuwar Darakta Aminu S. Bono

Fitaccen Darakta kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Aminu S. Bono ya rasu a ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba.

Mutuwar ta Bono ta girgiza masana’antar wanda aka jima ana jimamin rasuwar.

‘Yan uwa da abokan aikin marigayin sun nuna alhini matuka kan rasuwar Bono inda su ka ba da gudunmawa ga iyalansa don rage musu tradadi.

Darakta Abdul Amart ya gwangwaje iyalan da sabon gida yayin da kudin hayar gidan da su ke zaune ya kare a lokacin.

Har ila yau, Mawaki Dauda Rarara ya dauki nauyin karatun ‘ya’yansa gaba daya tun farko har karshe.

4. Mutuwar mawaki Mohbad a Legas

A ranar 12 ga watan Satumba, Matashin mawaki ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 27 wanda ya girgiza kasar baki daya.

Daga bisani an kama ma’aikaciyar asibitin da ta yi masa allurer ‘Tetanus’ inda rundunar ‘yan sanda jihar Legas su ka fara bincike kan mutuwar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu manyan nasarori 2 kan yan bindiga a Jihar Zamfara

Daga baya an tono gawar Mohbad bayan cece-kuce ya yi yawa kan zargin ba haka kawai ya mutu ba.

5. Rasa rayuka a lokacin zaben 2023

Akalla mutane fiye da 100 su ka rasa rayukansu a lokacin zaben shekarar 2023 kamar yadda hukumomi su ka tabbatar.

Rahoton ya tabbatar da cewa rasa rayukan sun faru ne tsakanin farkon watan Janaru zuwa 10 ga watan Maris, cewar Premium Times.

Zaben 2023 ya zo da kalubale masu tarin yawa wanda ya jawo rarrabuwar kawuna a kasar ganin yadda zaben ya koma bangaranci da addinanci.

6. Harin bam kan makiyaya a Nasarawa

Akalla makiyaya 27 ne su ka mutu yayin wani harin bam da aka sake musu a ruga a ranar 25 ga watan Janairun 2023, cewar Reuters.

Lamarin ya faru ne a jihar Nasarawa wanda makiyayan ke zargin harin sama ne da sojoji su ka yi wanda ya raunata da dama.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Kwankwaso ya kai ziyarar jaje game da harin bam a Kaduna, ya tura muhimmin sako

Daga bisani kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nemi a yi kwakkwaran bincike tare da gano makasudin harin tare da hukunta wadanda ke da hannu a ciki.

7. Rasuwar Ambasada Nuhu Bamalli

A ranar 20 ga watan Oktoba ce aka sanar da rasuwar Ambasada Nuhu Bamalli wanda shi ne ya ke rike da Magajin Garin Zazzau.

Marigayin ya kasance dan uwa ga Sarkin Zazzau da ke jihar Kaduna a Arewacin Najeriya.

An tabbatar da marigayin ya rasu ne a asibiti mai zaman kanshi a jihar Legas yayin da ya ke shirin tafiya kasar Morocco.

8. Rusau a Kano

Tun farkon hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan jihar ya fara rushe wasu gine-gine da ya ke ganin sun saba ka’ida.

Rusau din ya jawo cece-kuce daga bangarorin kasar baki da ma ‘yan kasuwa a jihar da su ke ganin hakan karya tattalin arzikin jihar zai yi.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali bayan gini ya ruguje kan mata da jaririnta mai kwanaki 9, mijin ya shiga yanayi

Daga bisani ‘yan kasuwar sun maka gwamnan a kotu inda a makon da ya gabata kotu ta umarci gwamnan ya biya diyyar biliyan 30.

Amma daga baya Abba Kabir ya amince da biyan biliyan uku kacal ga 'yan kasuwar a matsayin diyya.

Jerin rashe-rashe da aka yi a Kannywood

A wani labarin, an samu rashe-rashe a masana’antar Kannywood a cikin wannan shekara da muke ciki.

Legit Hausa ta jero muku rasa rayukar da aka yi tun daga mutuwar Samanja mazan fama har zuwa Aminu S Bono.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.