Jami’an Amurka Sun Kama Attajirin da Ake Ji da Shi a Najeriya Saboda Zambar $460m

Jami’an Amurka Sun Kama Attajirin da Ake Ji da Shi a Najeriya Saboda Zambar $460m

  • Mmobuosi Banye wanda aka fi sani da Dozy Mmobuosi a Najeriya ya shiga cikin matsala da hukumomin Amurka
  • SEC ta ce ‘dan kasuwan ya yi shekara da shekaru yana karyar cewa kamfaninsa ya mallaki miliyoyin da bai da su
  • Kamfanin Tingo Group Inc ya damfari mutane a duniya cewa ya ba $400m baya, ashe bai da sama da $50 a asusu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

United States - Makamanciyar hukumar SEC a Najeriya ta kasar Amurka ta ce kamfanin Tingo Group Inc ya yi karya kan dukiyarsa.

A lokacin da kamfanin na Tingo Group Inc ya yi ikirarin ya mallaki $461.7m, Business Day ta ce an gano $50 ne kurum a asunsunsu.

Mmobuosi Banye
An kama shugaban Tingo, Mmobuosi Banye a Amurka Hoto: www.investingport.com, www.middleeastmonitor.com
Asali: UGC

Mmobuosi Banye ya shiga hannu

Hukumar SEC ta kasar Amurka ta sanar da haka a ranar Litinin yayin da ta jefi Mmobuosi Banye da wasu kamfanoninsa da zargin zamba.

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan kasuwan da ake zargi da laifi a Amurka mutumin Najeriya ne. kwanakin baya aka ji wasu sun nemi ya tsaya takaran 'dan majalisar tarayya.

Ana binciken kamfanonin Tingo

Kamfanoninsa uku; Tingo Group Inc., Agri-Fintech Holdings Inc. da Tingo International Holdings Inc suna cikin wadanda ake tuhuma.

Techpoint Africa ta ce ana zargin Mmobuosi Banye da laifin yin karya wajen kambama kamfanoninsa domin ya damfari ‘yan kasuwa.

Hukumar ta SEC ta ce Dozy Mmobuosi yana yin hakan ne saboda ya yaudari masu hannun jari a fadin duniya, don haka za a hukunta shi.

Tingo: SEC za ta ceci masu hannun jari

Rahoton ya ce SEC tana so a dauki mataki ne domin hana ‘dan kasuwan yada bayanan karyar da za su iya jawo a damfari masu hannun jari.

A jawabin da hukumar ta fitar, an ji cewa ana zargin tun shekarar 2019 Mmobuosi yake karya a kan karfi da harkar kasuwancin kamfanoninsa.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu ya tsige shi, tsohon shugaban NSIB ya tona gaskiyar abinda ya faru yayin aikinsa

A bayanai, jawabai da takardun da Tingo Mobile Limited da Tingo Foods PLC su ka fitar, SEC ta ce an rika nuna abubuwan da ba gaskiya ba ne.

Yaudarar Dozy Mmobuosi Banye

A watan Maris na 2023, kamfanin Tingo Group ya ce ya mallaki tsabar kudi $461.7m a asusun bankinsa a Najeriya, alhali $50 kacal su ke da shi.

Yanzu an shigar da karar Mmobuos da wasu hudu a kotun kudancin Lardin New York

Juyin mulki da takunkumin Nijar

A makon jiya aka samu labari Africans Without Borders ta sa baki a rigimar sojojin da su ka yi juyin mulki a Nijar da kungiyar nan ta ECOWAS.

ECOWAS ta bukaci Africans Without Borders tayi kokari wajen ganin Mohammed Bazoum ya samu ‘yanci kafin a janye takunkumi kan Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel