Jami’in NSCDC da Ya Yi Suna Kan Katobarar ‘Oga at the Top’ Ya Samu Karin Girma, an Tuna Baya

Jami’in NSCDC da Ya Yi Suna Kan Katobarar ‘Oga at the Top’ Ya Samu Karin Girma, an Tuna Baya

  • Shem Obafiaye ya samu karin girma a hukumar NSCDC bayan tafka katobara shekaru 10 da su ka wuce a Najeriya
  • Shem shi ne jami'in da ya yi suna bayan furta kalmar 'My Oga at the top' yayin wani hara da gidan talabijin na Channels
  • Idan ba a mantaba, a shekarar 2013, Obafiaye lokacin da ya ke kwamandan hukumar a jihar Legas ya girgiza intanet da kalamansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jami'in hukumar NSCDC da ya yi kaurin suna bayan furta kalmar 'My oga at the top' ya samu karin girma.

Shem Obafiaye ya samu karin girman ne zuwa mukamin mataimakin babban kwamandan hukumar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tabbatar da barin Ciyamomi 21 da Kansiloli 239 ofisoshinsu, ya fadi dalili

Jami'in da ya yi suna a 2013 kan kalaman 'My Oga at the top' ya samu karin girma
Jami’in NSCDC da suna a 2013 ya samu karin girma. Hoto: @official_NSCDC.
Asali: Facebook

Wace katobara jami'in NSCDC ya yi?

Idan ba a mantaba, a shekarar 2013, Obafiaye lokacin da ya ke kwamandan hukumar a jihar Legas ya girgiza intanet da kalamansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obafiaye ya yi katobarar ce yayin hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirinsu ta safiya.

A yayin hirar Obafiaye ya ce:

"Yanar gizon ita ce...tsaya kadan..tsaya..oga na ne a sama kadai zai iya sanin yanar gizon.
"Ba zan iya fada maka dalla-dalla ba, ba zan iya fadan wani a nan kuma oga na a sama ya sake fadan wani daban ba."

Wane karin girma jami'in NSCDC ya samu?

Wannan katobarar ta jayo Obafiaye ya yi suna a Najeriya baki daya inda har ake amfani da shi wurin barkwanci.

Bayan shekaru 10, jami'in ya samu karin girma daga Gwamnatin Tarayya da sa hannun ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Ministan ya ce:

"A matsayi na na shugaban hukumomin NSCDC da kashe gobara da kuma shige da fice, na nada sabbin mataimakan kwamandojin NSCDC guda uku."

Jami'an NSCDC da DSS sun bai wa hamata iska

A wani labarin, An samu hargitsi yayin da aka bai wa hamata iska tsakanin jami'an NSCDC da na DSS a jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 4 ga watan Disamba a babban asibitin kwararru da ke Benin City.

Asali: Legit.ng

Online view pixel