An kama Faston dake fitar da makarai ta hanyar zukar nonon mata
- Malamin addinin Kirista ya shiga hannun jami'an tsaro saboda aikata badala ta hanyar fakewa da addini
- Faston na fitar da aljanu daga jikin mata ta hanyar zukar masu nono
- Ya ce yana zukar nonon matan ne domin fitar masu da aljanu da kuma warkar da su daga cututtuka
Wani limamin Coci, Fasto Raphael Obi, ya shiga hannun jami'an tsaro bayan samunsa da laifin fakewa da addini domin yada badala.
Fasto Obi, dan asalin jihar Enugu, yana tsotson nonon mata da sunan cire masu makarai ko warkar da su daga cututtuka.
Dubun Fasto Obi ta cika ne bayan da jami'an hukumar 'yan sanda na ofishin Idimu a karamar hukumar Alimosho ta jihar Legas suka kai wani samame gidansa.
'Yan sandan sun samu wasu wasu layu da kayayyakin tsibbu a gidan Faston. 'Yan sanda na cigaba da tsare Fasto Obi da komatsansa da aka samu a gidansa.
DUBA WANNAN: Ya nemi kotu ta raba aurensu saboda matar sa na amfani da al'aurar ta domin yin tsinuwa
Fasto Obi na jagorancin wata coci ne dake kan titin Abaranje a yankin Ikotun dake jihar Legas. Faston da Cocinsa na karkashin jagorancin shu'umin malamin addinin Kirista, Sharp Sharp, wanda ya yi suna wajen fakewa da addini domin tsibbu da cin mutuncin jama'a.
Hukumar 'yan sanda ta ce zata gurfanar da Fasto Obi da zarar ta kammala bincike.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Legas, Chike Oti, ya ce ba'a yi masa bayani kan lamarin ba, tare da daukan alkawarin sanar da manema labarai game da lamarin da zarar ya samu karin haske daga ofishin hukumar na Idimu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng