'Yan Sandan kasar Iran zasu dauki mataki kwakkwara ga matan da basu bin dokar saka Hijabi

'Yan Sandan kasar Iran zasu dauki mataki kwakkwara ga matan da basu bin dokar saka Hijabi

- Gwamnatin kasar Iran ta dauki kudurin hukunta duk matan da basa bin dokar saka hijabi

- Wasu mata a kasar sun tada zanga-zanga domin neman gwamnati ta cire dokar yawo da hijabin

- Dokar saka hijabin ta fara a kasar ne tun a shekarar 1979

'Yan Sandan kasar Iran zasu dauki mataki kwakkwara ga matan da basu bin dokar saka Hijabi
'Yan Sandan kasar Iran zasu dauki mataki kwakkwara ga matan da basu bin dokar saka Hijabi

'Yan sanda a kasar Iran za su murkushe duk wasu mata da suka nuna rashin amincewa da dokar saka Hijabi a kasar, in ji shugaban hukumar 'yan sanda na kasar Hussein Rahimi, yayi wannan jawabin ga manema labarai a ranar Talatar nan.

DUBA WANNAN: Metuh ya ce a shirye ya ke ya maidawa da gwamnati kudin da aka bashi na badakalar makamai

Ya ce, "Saka Hijabi wajibi ne ga matan Iran, sannan kuma duk wanda suka sabawa wannan dokar, hukuma zata dauki hukunci mai karfi a kansu. "Bai dace ba a ce za a bar mata su dinga yin abinda suka ga dama," in ji shi.

Tun daga watan Disamba, ana ta samun yawan adadin mata yana ta karuwa a kasar Iran, inda suke yin kira ga gwamnatin kasar da ta cire dokar yawo da hijabi da ta saka a kasar.

A yanzu dai haka a kalla mata 30 ne 'yan sanda suka kama kuma suke tsare dasu.

Wannan doka ta fara dai a kasar Iran tun a shekarar 1979, inda gwamnatin kasar ta saka doka daga kan yara mata 'yan sama da shekara 9 zuwa manyan mata da su dinga saka hijabi da kuma kaya masu yalwa, domin rufe gashin kansu da kuma surar jikin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng