Kano: EFCC Ta Gurfanar da Daraktan Kamfani Kan Zargin Hamdame Miliyan 21, an Fadi Yadda Su Ka Bace

Kano: EFCC Ta Gurfanar da Daraktan Kamfani Kan Zargin Hamdame Miliyan 21, an Fadi Yadda Su Ka Bace

  • An gurfanar da wani daraktan kamfanin Faris, Salisu Suleiman a gaban kotu kan zargin karkatar naira miliyan 21
  • Ana zargin Salisu da kuma kamfanin Faris da yin sama da fadi da kudaden da aka ware don siyan gas lita dubu 125
  • Babban daraktan yada labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale shi ya bayyana haka a yau Juma’a 15 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano Hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ta gurfanar da wani daraktan kamfani kan zargin karkatar da naira miliyan 21.

Ana zargin Salisu Sulaiman, daratan kamfanin Faris da kuma shi kanshi kamfanin kan zargin almundahana da makudan kudade, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi basarake har fadarsa sun dauki ransa a arewacin Najeriya

EFCC ta gurfanar da daraktan kamfani a Kano kan hamdame miliyan 21
Ana zargin Salisu da hamdame naira miliyan 21 na kamfani. Hoto: EFCC Nigeria.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Salisu da shi a Kano?

Babban daraktan yada labarai na hukumar, Dele Oyewale shi ya bayyana haka a yau Juma’a 15 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele ya ce an gurfanar da wanda ake zargin ne a ranar Talata 12 ga watan Disamba a gaban Mai Shari’a, Hadiza Sulaiman da ke babbar kotun jihar Kano.

Sanarwar ta ce:

“Ana zargin Salisu Suleiman, manajan kamfanin Faris da kuma kamfanin da badakalar naira miliyan 21 a ranar 15 ga watan Yunin 2021.
“Ana zargin an fitar da kudaden ne don biyan kudin gas lita dubu 125 a wurin aikinshi da ke karamar hukumar Nguru a jihar Yobe.
“Wannan laifi ya saba wa sashi na 308 na kundin laifuka da hukunci da kuma sashi na 309.”

Wane martani wanda ake zargin ya yi a Kano?

Kara karanta wannan

Dangote ya gwangwaje dalibai 199 da tallafin karatu don dogaro da kansu, ya fadi wasu shirye-shirye

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin bayan gama karanto masa tuhumar da ake yi a kansa, cewar Daily Nigerian.

Mai gabatar da kara, Aisha Tahar Habib ta bukaci kotun ta sanya ranar yanke hukuncin yayin da lauyan wanda ake kara, Mardiya Dawaki ta bukaci beli.

Mai Shari’a, Hadiza Suleiman ta umarci ci gaba da tsare wanda ake zargin tare da dage ci gaba da sauraran kara da kuma ba da beli, cewar The Herald.

EFCC ta daure ma’aurata kan almundahana

A wani labarin, Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu ma’aurata kan badakalar naira miliyan 140.

Ana zargin Aisha Salihu Rahab da mijinta, Abubakar Mahmoud da damfarar makudan kudaden a harkar kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.