EFCC ta na zargin wasu Ma’aurata da laifin sata a Jihar Akwa Ibom

EFCC ta na zargin wasu Ma’aurata da laifin sata a Jihar Akwa Ibom

A ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2020, jami’an hukumar EFCC na shiyyar Uyo, jihar Akwa Ibom su ka gurfanar da wasu ma’aurata da ake zargi da laifin sata.

Hukumar EFCC ta na tuhumar Gabriel Ikpenwa, da mai dakinsa Lillian Ikpenwa da kuma wata kungiya mai suna Easycash Multipurpose bisa zargin aikata laifuffuka biyu.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto dazu, laifuffukan da ake tuhumar ma’auratan da wannan kamfani su ne kutungwuilar sata da kuma karbar kudi ta hanyar karya.

An kai wannan kara ne gaban Alkalin babban kotun Akwa Ibom, Archibong Archibong. Mista Ikpenwa shi ne shugaban kungiyar Easycash Multipurpose da aka yi amfani da ita.

Gabriel Ikpenwa da Lillian Ikpenwa sun shiga matsala ne tun 2018, lokacin da wata mata, Maria Umana, ta kai kararsu gaban jami’an EFCC, ta ce sun karbe mata kudi masu yawa.

Maria Umana ta zuba kudi har N450, 000 a Easycash Multipurpose da nufin cewa za a rika ba ta N67, 500 a matsayin ribar ta a kowane wata, a karshe kudinta su ka makale.

KU KARANTA: Kotu ta ba EFCC da Ibrahim Magu rashin gaskiya a karar Olowonihi

EFCC ta na zargin wasu Ma’aurata da laifin sata a Jihar Akwa Ibom
Dakarun EFCC a bakin aiki Hoto: Twitter
Asali: Facebook

Umana ta shaidawa EFCC cewa an shafe shekaru biyar ba tare da ribar da aka yi mata alkawari ko ma akalla uwar kudinta sun fito ba, Wannan ya sa maganar ta kai gaban kuliya.

Da aka karantowa mutanen laifinsu, sun musanya cewa sun aikata wadannan laifuffuka.

Lauyan gwamnati da ya shigar da kara, N. Ukoha ya bukaci a sa ranar da za a saurari shari’ar, kafin nan kuma ya bukaci a daure wadanda ake tuhuma da laifi a gidan kurkuku.

Wanda ya tsayawa wadannan mutane biyu, C. I. Udoh, ya sanar da mai shari’a Archibong Archibong cewa an gabatar da takardu domin ayi belin iyalin Misis Ikpenwa.

Alkali Archibong ya bada belin Misis Lilian a kan Naira miliyan daya, an kuma samu wani mutum da zai tsaya mata. An dage wannan shari’ar sai cikin watan Disamban 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel