Mutum 12 Sun Mutu, 30 Sun Jikkata Bayan Tirela Ta Kife Yayin Haura Hawan-Kibo, An Bayyana Dalili

Mutum 12 Sun Mutu, 30 Sun Jikkata Bayan Tirela Ta Kife Yayin Haura Hawan-Kibo, An Bayyana Dalili

  • Ana cikin jimami yayin da mutane 12 su ka gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Plateau
  • Akalla mutane 30 ne su ka jikkata a hatsarin wanda ya rutsa da su a Hawan-Kibo da ke karamar hukumar Riyom a jihar
  • Kwamandan hukumar FRSC, Godwin Alphonsus ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a birnin Jos

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane 12 da jikkata wasu fiye da 30 a jihar Plateau.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a yankin Hawan-Kibo da ke karamar hukumar Riyom a jihar.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali bayan gini ya ruguje kan mata da jaririnta mai kwanaki 9, mijin ya shiga yanayi

Hatsarin mota ya yi ajalin mutane 12, fiye da 30 sun jikkata
Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 12 yayin da 30 su ka jikkata a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Yaushe hatsarin ya faru a Plateau?

Punch ta tababar cesa motar tirela ce makare da hatsi da kuma mutane ta kife yayin da ta ke haurawa a hanyar lokacin da abin ya afku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shaidar gani da ido ya ce bayan motar ta kife dukkan hatsin ya zube a ramuka tare da barin mutane matattu nan take, cewar Daily Post.

Kwamandan hukumar FRSC a jihar, Mista Godwin Alphonsus ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a Jos.

Wane martani hukumar FRSC ta yi?

Ya ce:

"Hatsarin ya afku ne da tsakar rana a jiya Alhamis inda tirelar ta kife a cikin rami yayin da take haura hawan titin.
"Motar na dauke da hatsi da kuma mutane yayin direban ya rasa birki lokacin da ya ke haura hawan.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

"Tun a lokacin, mutanen mu da ke Hawan-Kibo su ka isa wurin inda aka tabbatar mutane 11 sun mutu."

Alphonsus ya ce take su ka dauki mutane fiye da 30 da su ka jikkata zuwa asibiti mafi kusa don ba su kulawa na musamman, cewar Platinum Times.

Mutane 10 sun mutu a hatsarin mota

A wani labarin, akalla mutane 10 ne su ka mutu yayin wani mummunan hatsarin mota a jihar Kogi.

Hatsarin ya rutsa da magoya bayan jam'iyyar SDP ne yayin da su ke dawo wa daga taron siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.