Jerin Mutane 8 Da Suka Bada Taimakon Miliyan 700 Da Aka Kashe Masu Maulidi a Tudun Biri

Jerin Mutane 8 Da Suka Bada Taimakon Miliyan 700 Da Aka Kashe Masu Maulidi a Tudun Biri

  • Mutane da-dama sun yi wa al’ummar Tudun Biri ta’aziyyar kashe Bayin Allah kimanin 100 da aka yi
  • A sakamakon abin da sojoji suka kira kuskure, an samu asarar rayuka da dukiya mai yawa a garin
  • Wannan ya sa ‘yan siyasa, masu mulki da kungiyoyi suka rika aikawa da bada taimako a Tudun Biri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ana tsakiyar taron maulidi sojoji su ka harba bam-bamai, suka kashe mutane a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Su wanene suka bada gudumuwa a Tudun Biri?

1. Sanatocin Najeriya (N109m)

Duk Sanatocin kasar nan 109 sun yi abin a-yaba da su ka ware albashinsu domin a taimakawa mutanen da wannan hari ya shafa.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: ‘Dan Majalisar NNPP ya sa labule da Shugaba Tinubu a kan siyasar Kano

An rahoto cewa ‘yan majalisar dattawan za su hada N109m domin al’ummar Tudun Biri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. ‘Yan majalisar wakilai (N350m)

Alhassan Ado Doguwa ya sanar da cewa ‘yan majalisar tarayya za su bada gudumuwar N350m bayan kashe mutane kusan 100 da aka yi.

Hon. Ado Doguwa ya shaida haka lokacin da su ka ziyarci garin Kaduna a makon nan.

Sanusi da El-Rufai sun ziyarci Tudun Biri
Nasir El-Rufai da Muhammadu Sanusi II a Tudun Biri Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Instagram

3. Shugaban majalisar wakilai (N45m)

A matsayinsa na shugaban majalisa da kuma sauran abokan aikinsa daga Kaduna, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas sun yi alkawarin bada N45m.

4. Khalifa Muhammadu Sanusi II (N10m)

Ana rade-radin cewa Muhammadu Sanusi II ya ba mutanen wannan gari tallafin N10m a matsayinsa na Khalifan darikar Tijjaniya a Najeriya.

5. Nasir El-Rufai (N10m)

A rahoton da ba a tabbatar ba, an ce Nasir El-Rufai wanda ya ziyarci garin tare da Muhammadu Sanusi II shi ma ya bada gudumuwar N10m.

Kara karanta wannan

Shari’ar Kano: An Ja Kunnen Tinubu da Malamai 500 Suka Rokawa Abba Nasara a Kotu

6. Peter Obi (N5m)

‘Dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya ziyarci garin Tudun Biri domin yi masu ta’aziyyar rashin da su ka yi.

Peter Obi ya je asibitin Barau Dikko kuma ya bada gudumuwar N5m ga wadanda ke jinya kamar yadda Vanguard ta fitar da rahoto a baya.

7. Gwamnonin Arewa (N180m)

Bayan harin sojojin, Gwamnan Kwara ya ziyarci Kaduna a matsayin shugaban gwamnonin Arewa. Wata majiya ta ce ya bada kudi.

A taron gwamnonin Arewa, an tabbatar da cewa NGF ta bada gudumuwar N180m.

8. Jam’iyyatu Ansariddeen Attijjaniyya (N3.9m)

People Gazette ta ce kungiyar darika ta Jam’iyyatu Ansariddeen (Attijjaniyya) ta raba gudumuwar kayan wanki da tufafi N3.9m a Tudun Biri.

'Yan Tudun Biri sun kai gwamnati kotu?

Mukhtar Usman ya je kotu kamar yadda aka ji, ya ce Naira biliyan 33 al'ummar Tudun Biri su ke nema daga aljihun gwamnati a matsayin diyya.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun damke wasu jami’ai 3 za su yi gwanjon kayan gwamnati a Jihar Kano

Daga baya mutanen sun ce ba su shigar da kara a kotun tarayya mai zama a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng