Tudun Biri: Sanatoci 58 a Arewacin Najeriya Sun Dira a Kaduna, Sun Ba da Gudunmawa Mai Tsoka

Tudun Biri: Sanatoci 58 a Arewacin Najeriya Sun Dira a Kaduna, Sun Ba da Gudunmawa Mai Tsoka

  • Sanatoci daga yankin Arewacin Najeriya sun kai ziyara jihar Kaduna don jajantawa wadanda harin bam ya rutsa da su
  • Tawagar karkashin jagorancin Sanata Abdul Ningi da Abdul'aziz Yari sun mika sakon jaje da kuma gudunmawar miliyan 58
  • Wannan na zuwa ne bayan harin bam kan masu Maulidi a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Gamayyar Sanatoci a Arewacin Najeriya sun kai ziyara jihar Kaduna don jajantawa wadanda harin bam ya yi ajalinsu.

Tawagar karkashin jagorancin Sanata Abdul Ningi da Sanata Abdul'aziz Yari sun mika jajensu ga wadanda su ka rasa rayukansu, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ribadu da sanatocin arewa sun ziyarci Tudun Biri, sun nuna kwarin gwiwa kan hukumomin tsaro

Sanatocin Arewa sun dira a Kaduna yayin da su ka ba da gudunmawa kan harin Tudun Biri
Sanatoci 58 a Arewacin Najeriya sun ba da gagarumar gudummawa game da harin bam a Kaduna. Hoto: Media office of Senator Abdul'aziz Yari.
Asali: Original

Mene dalilin ziyarar sanatocin Kaduna?

Wannan na zuwa ne bayan harin bam kan masu Maulidi a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin ya yi ajalin mutane fiye da 100 yayin da dama su ka samu raunuka wanda su ke karbar kulawa a asibiti.

Shugaban tawagar, Abdul Ningi a madadin Sanatocin ya mika gudummawar naira miliyan 58 daga sanatoci 58 a yankin Arewa.

Wane gudunmawa sanatocin su ka bayar?

Rahotanni sun tattaro cewa wannan na daga cikin himmatuwar 'yan Majalisar wurin kawo dauki duk lokacin da aka samu iftila'i a yankin.

Yayin martaninshi, Sanata Yari mai wakiltar Zamfara ta Yamma ya yi Allah wadai da harin inda ya mika sakon jaje.

Ya ce:

"Mu na mika sakon yaje kan wannan iftila'i da ta afku a Kaduna, mu na addu'a ga wadanda su ka mutu da kuma iyalansu da fatan Allah ya bai wa wadanda su ka samu raunaka sauki."

Kara karanta wannan

El-Rufai da tsohon sarkin Kano sun ziyarci Tudun Biri kan bama-bamai da aka jefa wa Musulmai

Yari ya kuma ya yi kira ga jami'an tsaro da su dauki tsauraran matakai don kare faruwar hakan a gaba

Kungiyar CAN ta yi Allah wadai da harin Kaduna

A wani labarin, Kungiyar Kiristoci a Najeriya, CAN ta yi Allah wadai da harin sojoji kan masu Maulidi a Kaduna.

Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka ne bayan harin bam kan masu Maulidi inda ya bukaci a yi bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel