'Yan fashi sun tare motar banki, sun sace kusan biliyan N4

'Yan fashi sun tare motar banki, sun sace kusan biliyan N4

- Wasu tsagerun 'yan fashi sun tafka gagarumar satar da ta shiga cikin tarihin manyan sata da aka taba yi a duniya

- A ranar Juma'a ne 'yan fashi suka yi awon gaba da madarar kudi da suka kai Yuro miliyan tara a birnin Lyon da ke Kudu maso gabashin kasar Faransa

- Ba a samu labarin wata sata da ta kai wannan girma ba a tarihin kasar Faransa tun bayan satar Yuro miliyan 11.6 da hatsabibin barawo; Toni Musulin, ya yi a shekarar 2009

'Yan fashi sun yi awon gaba da madarar kudi kimanin Yuro miliyan tara a yau, Juma'a, a birnin Lyon da ke kudu maso gabashin kasar Faransa.

A cewar jami'an tsaro, 'yan fashin sun sace kudin ne bayan sun kai hari kan motar jami'an tsaro.

'Yan fashin sun budewa motar daukan kudi wuta a yayi da ta fito daga harabar wani banki na kasar Faransa reshen birnin Lyon.

'Yan fashi sun tare motar banki, sun sace kusan biliyan N4
'Yan fashi sun tare motar banki, sun sace kusan biliyan N4
Source: Facebook

Loomis security company, wani kamfanin harkokin tsaro, ya ce babu asarar rai sakamakon harin 'yan fashin, "amma an yi asarar makudan kudi da yawansu ya kai Yuro miliyan tara (kimanin dalar Amurka miliyan $10.7)," kamar yadda wani jami'i ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

DUBA WANNAN: Aikin N6bn: Rigima na kokarin kunno kai a tsakanin Dankwambo da gwamna Yahaya

Jami'in ya kara da cewa; "ma su laifin sun gaggauta barin wurin bayan sun kwashe kudin."

Wannan sata ta kasance mafi girma a cikin tarihin manyan sata da aka yi a kasar Faransa tun bayan fashin da hatsabibin barawo, Toni Musulin, ya yi awon gaba da Yuro miliyan 11.6 a shekarar 2009.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel