Tinubu Ya Kori Manyan Shugabannin Hukumomi 4, Ya Maye Gurbinsu Nan Take
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade inda ya sallami shugabannin hukumomin FAAN da NAMA
- Tinubu ya kori Kabir Mohammed a matsayin shugaban hukumar FAAN inda ya maye gurbinsa da Olabunmi Kuku
- Shugaban ya kuma sallami Tayyib Odunowo a matsayin shugaban hukumar NAMA tare da nada Umar Farouk a madadinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaba Tinubu ya sallami shugaban Hukumar Kula da Jiragen Sama (FAAN), Kabir Mohammed.
Shugaban ya kuma kori Tayyib Adetunji Odunowo a matsayin shugaban hukumar NAMA, cewar TheCable.
Yaushe Tinubu ya yi sabbin nade-naden?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Laraba 13 ga watan Disamba.
Kasa da awa 24 bayan Tinubu ya kori shugabannin hukumomi, ya sake korar daraktocin da Buhari ya nada
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ngelale ya ce Tinubu ya nada Olabunmi Kuku a matsayin wanda zai maye gurbin Kabir a hukumar FAAN.
Har ila yau, shugaban ya nada Umar Farouk a matsayin wanda zai maye gurbin Odunowo a hukumar NAMA.
Sabbin nade-naden za su fara aiki ne nan take kamar yadda sanarwa ta tabbatar, Legit ta tattaro.
Sauran wadanda aka sallama a hukumominsu
Sanarwar ta ce:
"Shugaba Tinubu ya amince da dakatarwa da sallama da kuma nadin shugabannin wadannan hukumomi da ke ma'aikatar kula da jiragen sama."
Shugaban ya kuma amince da nadin Alex Badeh Junior a matsayin shugaban hukumar NSIB bayan ya sallami Akinola Olateru a matsayin shugaban hukumar.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Tinubu ya sallami shugaban hukumar NIMET, Mansur Bako Matazu inda ya maye gurbinsa da Charles Anosike a matsayin babban daraktan hukumar.
Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Ondo
A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake shiga tsakani kan rikicn siyasa a jihar Ondo da ta ki ci ta ki cinyewa.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke saka baki amma a karon farko da ya shiga ba a samu abin da ake bukata ba.
Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari a jihar tun bayan rashin lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu.
Asali: Legit.ng