‘Yan Shi’a Sun Taso Sojoji, Sun Nemi Hukunta Sojojin da Suka Kashe 'Yan Maulidi
- ‘Yan Islamic Movement in Nigeria (IMN) sun shirya zanga-zanga saboda kashe mutane da aka yi a garin Tudun Biri
- Kungiyar mabiya Shi’ar ta kai korafi zuwa NRHC domin a binciki yadda sojoji su ka hallaka fararen hula a wajen maulidi
- Sheikh Sidi Mainasara Sokoto ya rubuta takarda ga hukumar NRCH domin a hukunta sojojin da ke da laifin kashe rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Kungiyar IMN ta mabiya Shi’a, su ka nuna fushinsu a kan kashe mutane da sojoji su ka yi a garin Tudun Biri a jihar Kaduna.
A ranar Litinin kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto, mabiya kungiyar addinin musuluncin su ka fara shirya zanga-zangar lumuna.
Yadda 'yan shi'a su kayi zanga-zanga
An fara gudanar da zanga-zangar ne a kusa da ofishin hukumar PCC mai sauraron korafin jama’a a unguwar Maitama a birinin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar lumanar sun cigaba da tattakinsu zuwa ofishin hukumar NRHC, inda su ka gabatar da korafi a kan sojojin Najeriya.
IMN ta kai kara wajen Shugaban NRHC
Sheikh Sidi Munir Mainasara Sokoto ya sa hannu a wasikar da kungiyar ta IMN ta mikawa shugaban NRHC na kasa, Anthony Ojukwu.
Kungiyar ta bukaci Anthony Ojukwu ya tursasa gwamnatin tarayya tayi bincike na musamman a game da abin da ya faru a Tudun Biri.
Shi'a za ta sa a hukunta Sojojin Najeriya?
Bayan binciken, wasikar Sheikh Sidi Mainasara Sokoto ta nuna ana so a gurfanar da duk sojan da ke da hannu wajen kashe Bayin Allah.
The Cable ta ce kungiyar IMN ba ta gama yarda cewa abin da ya faru kuskure ba ne, ta ce dole gwamnati ta biya dangogin diyyar rayuka.
IMN ta ce ba wannan ne karon farko da aka fara wannan danyen aiki a Najeriya ba, ta ce ya kamata duk mai hankali ya yi tir da lamarin.
Wasikar 'Yan kungiyar IMN
"Dole a fito a bukaci ayi wa mutanen garin Tudun Biri adalci. A gano wadanda su ka yi aika-aikan nan, ayi bincike kuma a gurfanar da su.
A shirya bincike a gano abin da ya faru, adadin wadanda aka kashe ko masu rauni, asarar da mutanen Tudun Biri su ka yi a sanadiyyar haka."
- Kungiyar iMN
Majalisar Kano ta ce a kama Baffa Hotoro
Har kiristoci sun yi ta’aziyya amma an ji wasu malamai kamar Baffa Hotoro da Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi sun yi kalamai masu zafi.
A dalilin haka majalisar dokokin Kano ta bukaci gwamnati, Hisbah da majalisar Shura ta dauki mataki kan Hotoro kuma a hukunta shi.
Asali: Legit.ng