Sanusi ga ECOWAS: Ba a Sa Takunkumi ga Israila ba, Amma Kun Hana Nijar Abinci da Lantarki

Sanusi ga ECOWAS: Ba a Sa Takunkumi ga Israila ba, Amma Kun Hana Nijar Abinci da Lantarki

  • Muhammadu Sanusi II ya roki shugabannin kungiyar ECOWAS su janye takunkumin da aka maka a kan Kasar Nijar
  • Sarkin Kano na 14 bai goyon bayan yadda ake azabtar da jama’a a Nijar saboa sojoji sun hambarar da mulkin farar hula
  • Sanusi II ya ce duk yadda Israila ta ke kashe Larabawan Falasdin, kasashen Yamma ba su kakaba mata takunkumi ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yi magana yayin da shugabannin kasashen Afrika ta yamma su ka zo taron ECOWAS.

A ranar Lahadi, aka samu labari shugabannin kungiyar ECOWAS sun yi zama a birnin Abuja domin batun juyin mulkin da aka yi a kasar Nijar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Sanusi II
Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga ECOWAS Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga shugabannin su cire takunkumin da aka kabawa mutanen Nijar saboda an kifar da gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da yake yawo a Facebook, Muhammadu Sanusi II ya ce al’ummar Nijar ta na shan wahala sakamakon halin da makwabta su ka jefa ta.

Bayan kokarin da ya yi kwanakin baya a Yamai, an ji Sanusi II yana mai cewa baya ga rashin lantarki, an hana a kai abinci da magunguna kasar.

ECOWAS: Jawabin Muhammadu Sanusi

"Shugabannin kungiyar ECOWAS suna taro a Abuja, muna fata kuma muna rokon Allah su daga takunkumin da aka daura a kan kasar Nijar.
Wannan kasa, kasa ce ta ‘yanuwa kuma su na cikin wahala. Wata da watanni babu lantarki, an hana abinci, an hana magani shiga.
Mutanen da mu ke yin wannan domin su, muna kallon yadda su ke yi a Israila, ana kashe Falasdinawa, ana kona asibitoci.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi maganar kisan masu Maulidi, ya fadi nasarar farko da aka samu

Babu wani juyin mulki da aka yi a Nijar da illarsa ta kai illar da Yahudawa su ke yi wa Larabawa a Israila a yanzu ba, amma ba a sa masu takunkumi ba.

- Muhammadu Sanusi

Sanusi II ya yi maganar zaluncin Israila

Sanusi II ya ce bai kamata shugabannin kasashen Afrika ta yamma su zake a game da batun damukaradiyya har fiye da turawan yamma ba.

Idan da gaske ake yi, Khalifan Tijjaniyan ya ce a fara kakaba takunkumi a kan kasar Israila wanda ta yanke wuta, ta ke kashe mutane a Gaza.

Ka san asarar da ake yi saboda rufe iyakar Nijar?

‘Yan kasuwa sun yi watanni ana rasa kudi saboda toshe hanyar kasuwancin Najeriya da ketare. AFFPON ta ce N13bn ake rasawa duk mako.

Kungiyar ‘Arewa Economic Forum’ ta ce asara ta kusan Naira Biliyan 1.8 ake yi a kullu- yaumin, ta roki kungiyar ECOWAS ta sassautawa Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel