'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Kan Tawagar Yan Kwallon Jihar APC, Sun Yi Musu Mummunar Illa

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Kan Tawagar Yan Kwallon Jihar APC, Sun Yi Musu Mummunar Illa

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari kan tawagar ƙungiyar kwallon kafa ta jihar Ondo, Sunshine Stars a hanyar zuwa buga wasa
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun harbi jami'i ɗaya, sun jikkata mai horarwa da ƴan wasan ƙungiyar
  • Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ondo ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ya faru a wurin da ba ya karkashin ikonta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun farmaki ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Sunshine Stars da ke Akure, jihar Ondo.

‘Yan bindigar da yawansu ya kai biyar sun yi wa ‘yan wasan kwanton bauna ne a kan titin Ore/Benin a lokacin da suke hanyar zuwa buga wasan waje.

Kara karanta wannan

An kuma: Yan bindiga sun kai sabon hari, sun yi garkuwa da ɗaliban jami'ar tarayya a arewa

Yan bindiga sun farmaki motar tawagar Sunshine Stars
Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Kwallon Kafa Ta Jihar Ondo, Sun Harbi Jami'ar Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, tawagar yan wasan zasu kara da ƙungiyar Bendel Insurance na Benin, a hanyar zuwa wasan ne lamarin ya rutsa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa maharan sun harbi wani jam'in kungiyar Sunshine Stars a ciki amma har kawo yanzu ba a faɗi bayanan wanda aka harba ba.

Haka nan kuma mai horar da tawagar kwallon kafan, Seun Betiku, da wasu abokan aikinsa sun samu rauni sakamakon harin.

Maharan sun yi wa yan wasan illa

Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar Sunshine Stars Football Club, Michael Akintunde, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar salula.

Ya ce tawagar ƴan wasan na hanyar zuwa taka wasan mako na 13 a gasar cin kofin Premier na nan gida Najeriya a Benin lokacin da ƴan bindiga suka kawo harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari ƙauyuka 4 a Arewa, sun kashe rayuka da yawa

A rahoton The Nation, Mista Akintunde ya ce:

"An harbi ɗaya daga cikin ma'aikatan mu a harin, mai horas wa da wasu ma'aikatan ƙungiyar kwallon ƙafa ciki harda ƴan wasa sun ji raunuka."
"Har sai da jami'an hukumar kiyaye haɗurra suka shiga tsakani, suka taimaka wajen ceto jami'anmu da suka ji rauni da wanda aka harba zuwa asibiti mafi kusa."

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce harin ya auku a inda ba ta da hurumi.

Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Mataki Kan Sojoji da Suka Jefa Bam a Taron Musulmi

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin hukunta duk wanda aka gano da laifi a harin bama-baman ƙauyen Tudun Biri.

Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne ta bakin Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawaga zuwa Kaduna don jajantawa waɗanda abun ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel