“Sha’awa Ce”: Yadda Farfesan Jami’ar ABU Ya Kama Aikin Walda a Matsayin Sana'a

“Sha’awa Ce”: Yadda Farfesan Jami’ar ABU Ya Kama Aikin Walda a Matsayin Sana'a

  • Farfesa Kabir Ahmed Abu-Bilal na jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, jihar Kaduna yana da tarin digigir a bangaren ilimi
  • Sai dai kuma, domin samun na dogaro da kai, masanin ya kama sana'ar walda inda ya bude shago a gefen hanya
  • Farfesan na bangaren injiniyan lantarki ya ce dama yana sha'awar aikin walda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Zaria, jihar Kaduna - Wani farfesan jami'ar Najeriya, Kabir Ahmed Abu-Bilal, ya dauka hankali bayan ta bayyana cewa aikin walda yake yi.

Farfesan mazaunin Kaduna ya ce abun da yake samu daga shagonsa a wata ya ninka albashinsa na wata a matsayin farfesa, yana mai cewa wannan na daya daga cikin dadin da ke tattare da aikin hannu.

Kara karanta wannan

Gagaruman abubuwa 3 da za su faru a 2024, malamin addini ya yi hasashe

Farfesan ABU ya kama sana'ar walda
“Sha’awa Ce”: Yadda Farfesan Jami’ar ABU Ya Kama Aikin Walda a Matsayin Sana'a Hoto: Phynart Studio
Asali: Getty Images

'Ina samun riba daga sana'ar walda': Farfesa

Da yake zantawa da Daily Trust, farfesan na bangaren injiniyan lantarki, ya ce dama can yana da sha'awar aikin walda kuma hakan wata hanya ce ta amfani da baiwar da Allah ya yi masa wajen dogaro da kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya yi bayanin cewa ya fara sha'awar aikin hannu ne daga bangaren karantarwarsa, inda yake koyar da dalibai bayanai a rubuce da aikace.

Kalamansa:

"Tunda muna mu’amala da na’urorin lantarki ne a lokacin darussanmu, cikin sauki na fara sha’awar aikin walda kuma na fara yi tare da wasu dalibaina, wadanda suka fi ni kwarewa a bangaren yinsa a aikace.
"Saboda haka, na koyi karin aikin daga wajensu sannan na hada da wanda na ke da shi, wanda hakan ya sa na fahimci sana'ar cikin sauri."

Bugu da kari, malamin na jami'ar ABU ya bayyana cewa, a yayin taron karawa juna sani na jami'ar, ayyuka masu zaman kansu suka fara shigowa, amma mahukuntan makarantar sun samu labari sannan suka hana yin aiki a waje.

Kara karanta wannan

Hawaye da tsoro yayin da gwamnan APC ya tsige ma'aikata masu yawan gaske

Ya zargi jami'ar da rashin hada kai da shi da sauran mutane "domin samar da wasu kudaden shiga ga tsangayar da ma'aikatar gaba daya".

Ya tuna cewa a yajin aikin karshe da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi a lokacin da aka hana malaman jami’o’in albashi na tsawon watanni, yajin aikin bai yi tasiri a wajensa ba.

Ya ce:

“Harma wasu abokan aikina suna zuwa nan don aron kudi saboda sun koyi darasi. Wasu kuma suna zuwa neman taimako saboda rashin biyan albashi."

Jami'ar Gombe ta karrama dattijo

A wani labarin, mun ji cewa jami'ar jihar Gombe ta karrama dan Najeriya mai kirkiran abubuwa, Injiniya Hadi Usman da digirgir a bangaren kimiyya.

A cewar babban mai ba gwamnan jihar Gombe shawara ta musamman kan harkokin labarai, Safianu Danladi Mairiga a dandalin X, an bai wa Usman shaidar digiri a bikin yaye dalibai na jami'ar jihar Gombe da aka kammala kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel