Gaba da kowa: Jami'ar ABU Zaria za ta buɗe makaranta 25 ga Janairu

Gaba da kowa: Jami'ar ABU Zaria za ta buɗe makaranta 25 ga Janairu

- Daga karshe, Jami'ar ABU Zaria ta sanya ranar 25 ga watan Janairu domin buɗe makaranta

- Sai dai jami'ar ta shirya wani tsari da za ta bi wajen koyar da dalibai a wannan lokaci da ake ciki na annobar korona

- Har ila yau hukumar jami'ar ta sanar da wasu tanadi da ta shirya domin taimakawa cibiyar lafiyarta da abubuwan bukata don kare kai

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Ahmadu Bello University (ABU), Zaria ta sanya ranar 25 ga watan Janairu a matsayin ranar komawar dalibai makaranta.

Daraktan harkokin jama’a na jami’ar, Awwal Umar, ne ya bayyana hakan, cewa an yanke shawarar ne a taron hukumar gudanarwa ta makarantar karo na 501.

KU KARANTA KUMA: Na koma APC ne domin na gina rayuwar ‘ya’yana, In ji Sanata Abbo

Gaba da kowa: Jami'ar ABU Zaria za ta buɗe makaranta 25 ga Janairu
Gaba da kowa: Jami'ar ABU Zaria za ta buɗe makaranta 25 ga Janairu Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Sai dai Umar ya ce dawowar daliban zai zo a rukuni-rukuni inda dukkanin daliban dake a shekararsu ta karshe za su fada a rukunin farko, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewa: “Daliban aji daya da na aji biyu da dukkanin daliban likitanci suma za su fada a rukunin farko. Dukkanin daliban digiri na biyu za a dunga daukarsu darasi ta yanar gizo."

Jawabin ya bayyana cewa sauran rukunin daliban za su kasance a rukuni na biyu, kamar yadda yake a kalandar makarantar.

Sai dai ya ce ranar 25 ga watan Janairun da aka sanar a matsayin ranar komawar daliban na iya sauyawa gwargwadon hali na wani umarni da ka iya fita a kowane lokaci daga bakin Gwamnatin Tarayya ko kuma Gwamnatin Jihar Kaduna.

Umar ya ce hukumar jami’ar za su yi amfani da abunda suke da shi a hannu wajen taimaka wa bangaren kiwon lafiya na makarantar da kayan kariya da kuma samar da wajen kula da duk wani rashin lafiya da ke da nasaba da korona.

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari bai kawo karshen rashin tsaro ba

A gefe guda, mun ji cewa a ranar Litinin, 11 ga watan Junairu, 2020, gwamnatin tarayya tace za ta duba maganar bude makarantu da ta sa cewa za ayi a ranar 1 ga watan nan.

Gwamnatin kasar ta ce hakan ya zama dole ne a sakamakon cutar COVID-19 da ta dawo da karfinta.

Jaridar Punch ta ce mai girma Ministan ilmi na kasa, Malam Adamu Adamu, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida jiya a birnin Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel