Tudun Biri: Kungiyar CAN Ta Yi Martani Game da Harin Bam Kan Masu Maulidi a Kaduna, Ta Tura Bukata

Tudun Biri: Kungiyar CAN Ta Yi Martani Game da Harin Bam Kan Masu Maulidi a Kaduna, Ta Tura Bukata

  • Yayin da ake jimamin mutuwar masu Maulidi a Kaduna, Kungiyar CAN ta yi Allah wadai da harin bam din da sojoji su ka kai
  • Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta fifita kare rayukan al’umma
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu Kiristoci kan wannan jaje na kungiyar Kiristoci CAN

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja- Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta tura sakon jaje ga al’ummar Musulmi game da harin bam kan masu Maulidi, cewar Tribune.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar, Daniel Okoh inda ya ce harin abin takaici ne.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Kungiyar CAN ta yi Allah wadai da harin bam a kan masu Maulidi
Kungiyar CAN ta yi martani kan harin bam a Kaduna. Hoto: Daniel Okoh.
Asali: Facebook

Wane martani CAN ta yi kan harin na Kaduna?

Okoh ya jajantawa iyalan wadanda su ka mutu inda ya yi addu’ar samun sauki ga sauran wadanda su ka samu raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kuma shawarci rundunar sojin da ta tabbatar da ingancin bayanan sirri kafin kai hari a ko wane hali.

Okoh ya ce:

“Mu na rokon jami’an soji da su mutunta kare lafiyar ‘yan kasa da kuma tabbatar da kauce wa irin wannan iftila’i.
“A kokarin dakile faruwar hakan a gaba, ya kamata rundunar ta taka tsan-tsan wurin samun bayanan sirri don kaucewa afkuwar haka a gaba.
“CAN ta himmatu wurin bai wa Gwamnatin Tarayya goyon baya a fada da ta’addanci, mu na fatan za ta yi kokarin kare rayukan jama’a.”

Wace shawara CAN ta bayar?

Har ila yau, kungiyar ta yi kira ‘yan siyasa da shugabannin addinai da su kai zuciya nesa don gudun faruwar wani tashin hankali a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun koma kashe fararen hula: Sanata Sani ya ce babu kuskure a harin Kaduna

Wannan na zuwa ne bayan kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a ihar Kaduna.

Harin bam din ya yi ajalin mutane fiye da 100 wadanda ke bikin Maulidi a daren ranar Lahadi 3 ga watan Disamba.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu Kiristoci kan wannan jaje na kungiyar CAN.

Mary Amos ta ce wannan ya yi dai-dai ganin yadda Musulmi da Kirista ke bukatar hadin kai a wannan lokaci da ake da rarrabuwar kayuka.

Mshelia Dauda ya ce:

"Ina taya Musulmai alhinin rashin 'yan uwansu, ubangiji ya jikansu ya sa sun huta."

Jingir ya yi Allah wadai da harin Kaduna

A wani labarin, Shugaban Majalisar Malamai ta kungyar Izalar Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna.

Jingir ya ce wannan abin takaici ne yadda aka hallaka bayin Allah saboda ganganci na rundunar sojin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.