Kashe ‘Yan Maulidi: Shettima Ya Jero Ayyukan da Tinubu Zai Yi wa Mutanen Tudun Biri

Kashe ‘Yan Maulidi: Shettima Ya Jero Ayyukan da Tinubu Zai Yi wa Mutanen Tudun Biri

  • Kashim Shettima da tawagar gwamnatin tarayya sun kai ziyarar ta’aziyya zuwa kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna
  • Mataimakin shugaban kasar ya yi wa al’umma jajen tsautsayin da ya rutsa da wasu a wajen taron maulidi
  • Shettima ya fitar da jawabi cewa za a kawo ayyuka da tsare-tsare domin a tallafawa mutanen Tudun Biri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Kashim Shettima ya ce gwamnatin tarayya za ta sake gina garin Tudun Biri bayan harin bam ya yi mummunan barna a makon jiya.

Mataimakin shugaban kasa watau Kashim Shettima ya ziyarci inda abin ya faru, Premium Times ta ce ya kuma shaida masu niyyarsu.

Tudun Biri
Kashim Shettima ya ziyarci mutanen Tudun Biri Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

Matakan da gwamnati ta dauka a Tudun Biri

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi maganar kisan masu Maulidi, ya fadi nasarar farko da aka samu

Sanata Kashim Shettima ya ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya umarci a fara aiwatar da tsarin Fulako a garin Tudun Biri a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka, gwamnatin tarayya za ta gina gidaje, dakunan shan magani, asibitin dabbobi a sakamakon masifar da ta aukawa kauyen.

Kashim Shettima ya ce akwai tsare-tsaren tallafawa al’umma da za a fito da su, sannan za a kawo wuta mai amfani da hasken rana.

Rage zafin rasuwar mutane 85 a Tudun Biri

Duk gwamnati za tayi wannan ne domin rage radadin mutane 85 da sojoji su ka kashe.

An rahoto Mataimakin shugaban kasar yana cewa ragowar wadanda su ka ji rauni suna asibitin koyon aikin Barau Dikko ana kula da su.

Sanata Shettima ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fito ta bakin Stanley Nkwocha.

Kara karanta wannan

"Ba ku ci bulus ba" Shugaba Tinubu ya ɗauki mataki mai tsauri kan sojojin da suka jefa bam a Kaduna

Stanley Nkwocha ya ce an umarci hukumar NEMA ta shiga kauyen Tudun Biri domin taimakawa wadanda su ke bukatar agaji a yau.

Tinubu zai fito da tsarin Fulako

Sauran jihohin da za su amfana da tsarin Fulako da za a kaddamar a watan gobe sun hada da Sokoto, Kebbi, Zamfara da kuma Katsina.

Har ila a cikin jihohin akwai Neja da Benuwai wanda Shettima ya ce an kara da gan-gan.

Mun koyi darasi a Tudun Biri - Sojoji

Ana da labari cewa daga yanzu DHQ ta ce sojojin Najeriya za su rika tabbatarwa dari-bisa-dari kafin su kai ga sakin bama-bamai a wuri.

Manjo Janar Edward Buba ya ce ba za a sake samun irin haka ba, kuma ya musanya zargin cewa sojoji suna yakar Arewa ne ta bayan-fage.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng