An Yanke Wa Wani Dan Jihar Zamfara Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe Abokinsa Kan Naira 100
- Wata babbar kotun jiha da ke da zamanta a Zamfara ta yanke wa wani dan jihar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe abokinsa
- An rawaito cewa Anas ya kashe abokinsa a watan Yunin shekarar 2017 bayan rikici ya barke tsakaninsa da Mukhtar kan Naira dari
- Haka zalika, babbar kotun ta yanke hukuncin kisa kan wani Sadiqu bisa samun sa da laifin yunkurin fashi da makami a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Zamfara - Babbar kotun jihar Zamfara ta yankewa wani Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe abokinsa kan Naira dari.
A watan Yuni 2017 ne aka gurfanar da Dahiru gaban kotun bisa zarginsa da dabawa abokinsa Shamsu Ibrahim wuka, da ya yi silar mutuwarsa.
Mutane biyu da kotu ta yanke wa hukuncin kisa a rana daya
Da ya ke yanke hukunci, shugaban kotun, mai shari'a Mukhtar Yusha'u, ya ce ya yanke wa Dahiru hukuncin ne bayan jin ta bakin kowanne bangare, Radio Nigeria ya ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bayan jin ta bakin kowanne bangare, na yanke wa Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda sashe na 221 da ke cikin kundin final ya tanadar."
A cewar sa.
A wani labarin makamancin wannan, mai shari'ar ya kuma yanke wa wani Sadiqu Abubakar hukuncin kisa kan yunkurin fashi da makami a karamar hukumar Bungudu da ke jihar.
An yanke wa Sadiqu hukuncin kisa bisa farmakar wani dan kasuwa a kauyen Runji wanda ya damke dan fashin tare da mika shi hannun 'yan sanda, Legit ta ruwaito.
Yusha'u ya ce bayan jin ta bakin kowanne bangari dangane da shari'ar, ya yanke wa Sadiqu Abubakar hukuncin kisa karkashin sashi na 221 da ke kunshe a kundin final.
Kotu ta garkame lebura wata 7 kan satar agwagin turawa a Filato
A wani labarin da Legit Hausa ta kawo a ranar Alhamis, wata kotu a Jos ta garkame wani lebura dan shekara 41 mai suna Adrew Enoch a gidan gyaran hali na tsawon wata bakwai kan satar agwagin turawa.
Mai shari'a Anas Mohammed ya aike da Enoch gidan gyaran halin bayan da ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
Asali: Legit.ng