Kotu Ta Garkame Lebura Wata 7 a Gidan Gyaran Hali Kan Satar Agwagi Guda 3 a Filato

Kotu Ta Garkame Lebura Wata 7 a Gidan Gyaran Hali Kan Satar Agwagi Guda 3 a Filato

  • Wata kotu a garin Jos, jihar Filato ta garkame wani lebura mai shekara 41 da haihuwa kan satar agwagin turawa uku da kashe su
  • Mai shigar da kara ya tabbatar wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya shiga wani gida a watan Agusta, inda ya saci agwagin
  • Bayan da mai laifin ya amsa laifin da ake tuhumarsa, mai shari'a Mohammed ya kulle shi wata bakwai da zabin biyan tarar naira dubu saba'in

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jos, jihar Filato - A ranar Alhamis ne wata kotu a Jos ta garkame wani lebura dan shekara 41 mai suna Adrew Enoch a gidan gyaran hali na tsawon wata bakwai kan satar agwagin turawa.

Kara karanta wannan

Kasafin Tinubu ya fusata Arewa, ba a ware sisi domin aikin wutan Mambilla a 2024 ba

Mai shari'a Anas Mohammed ya aike da Enoch gidan gyaran halin bayan da ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Kotu ta garkame barawon agwagin turawa a Filato
Bayan samunsa da aikata laifin da ake tuhumarsa, kotu ta kulle lebura wata bakwai gidan gyaran hali a jihar Filato. Hoto: Federal High Court
Asali: UGC

Sai dai kuma Mohammed ya ba mai laifin zabin biyan tarar naira dubu saba'in, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Enoch ya aikata laifin da ake tuhumarsa

Ya kuma umurce shi da ya biya naira dubu casa'in ga wanda ya shigar da karar matsayin diyya, ko kuma gaza biyan kudin zai sa ya kara yin wata daya a gidan yarin.

Tun da fari dai jami'i mai shigar da kara, Sifeta Labaran Ahmed, ya shaidawa kotun cewa wani Ishaiah Habi ne ya kai karar wanda ake zargin ofishin 'yan sanda a ranar 17 ga watan Agusta.

Sufetan 'yan sandan ya ce Andrew ya shiga gidan mai karar inda ya saci agwagin turawan guda uku.

Kara karanta wannan

Kaico: Shekaru biyar da ritaya, sufetan 'yan sanda ya koma barace-barace a titi

A cewar sa, wanda ake zargin ya kashe agwagin kafin a kama shi.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya ruwaito Ahmed na cewa laifin da Enoch ya aikata ya saba da dokar kundin final na jihar Filato.

Yan sanda sun damke masu laifi 130 a Katsina, sun gurfanar da 61

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda ta sanar da nasarar da dakarunta suka samu na afke masu laifi 130 a jihar Katsina.

A cikin wata daya rundunar ta samu wannan nasarar kamar yadda kakakin rundunar na Katsina ya bayyana, Legit ta ruwaito.

Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan fashi 38, masu kisan kai 16, da sauransu, kuma ta kubutar da mutum 69.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel