Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020

Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020

Bayanai sun nuna cewa a kalla mutum tara aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke yankin arewacin Najeriya daga farkon shekarar 2020 zuwa watan Augusta.

Kamar yadda takardun kotu daban-daban suka bayyana kuma BBC ta gani, an yanke wa mutanen hukuncin kisan bayan samunsu da aka yi da wasu manyan laifuka.

Bakwai daga cikinsu sun samu hukuncin kisan bayan da aka kama su da laifin kisan kai, daya daga ciki ya yi wa karamar yarinya fyade sai guda daya da yayi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Idan za mu tuna, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dauka alkawarin saka hannu a kan takardar kashe Yahaya Sharif-Aminu, matashin da aka kama da laifin batanci ga Annabi.

Ga jerin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano daga watan Janairun shekarar nan zuwa watan Augusta.

1. Ali Abdullahi: A ranar 11 ga watan Fabrairun da ta gabata, wata kotu a jihar Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

2. Yakubu Dalha: Wata kotu mai lamba shida a birnin Kano ta yanke masa hukuncin kisa sakamakon kama shi da tayi da laifin kisan kai a ranar 3 ga watan Maris na wannan shekarar,

3. Abdullahi Isyaku: Babbar kotu a jihar Kano ta kama shi da laifin kisan kai, lamarin da yasa ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 16 ga watan Maris.

4. Mujahid Sa'id: Wata kotu mai lamba 13 ta kama Mujahid da laifin kisan kai a ranar 24 ga watan Maris. Hakan yasa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020
Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon ranar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban

5. Naziru Ya'u: An yanke wa Naziru Ya'u hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 26 ga watan Yuni bayan kama shi da aka yi da laifin kisan kai.

6. Shehu Ado Shehu: Wata kotu mai lamba 6 ta yankewa Shehu Ado hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 26 ga watan Yuni bayan kama shi da tayi da laifn kisan kai.

7. Isah Auta: An yanke wa Auta hukuncin kisa a ranar 29 ga watan Yunin 2020, bayan kama shi da aka yi da laifin kisa. Za a kasheshi ta hanyar rataya.

8. Yahaya Aminu: babbar kotun shari'ar Musulunci da ke Kano ta kama Yahaya Aminu da laifin batanci ga Annabi Muhammadu.

A ranar 10 ga watan Augustan 2020, kotun ta yanke wa matashin mawakin hukunci kisa ta hanyar rataya.

9. Mati Abdu: Babbar kotun shari'ar Musulunci da ke birnin Dabo ce ta kama tsohon da laifin fyade. Ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa a ranar 12 ga watan 12 ga watan Augusta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel