Abba vs Gawuna: ’Yan Sanda Sun Roki Malaman Addini Su Dage da Yin Wa’azi Kan Tada Tarzoma a Kano

Abba vs Gawuna: ’Yan Sanda Sun Roki Malaman Addini Su Dage da Yin Wa’azi Kan Tada Tarzoma a Kano

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta nemi malaman addini da su daura damarar yinmabiyansu wa'azi kan muhimmancin zaman lafiya a jihar
  • Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Huseini Gumel ne ya bayyana hakan a ganawarsa da malaman addini na jihar gabanin hukuncin Kotun Koli
  • Gumel ya ce hukumar ba za ta yi kasa a guiwa wajen kama wa tare da hukunta duk wanda ta samu da yunkurin tayar da tarzoma a jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Huseini Gumel, kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Kano, ya roki malaman addini da su dage da yi wa mabiyansu wa'azi kan muhimmancin zaman lafiya a jihar.

An samu tashin hankula a hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben jihar Kano da Kotun Daukaka Karfa suka yanke na korar Gwamna Abba Yusuf daga gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Waye zai yi nasara a kotu? Jigon siyasa ya hango abin da zai faru a shari'ar Abba da Gawuna

Rundunar 'yan sanda ta gana da malaman addini a jihar Kano
Rundunar 'yan sanda ta ce ba za ta gaza wajen hukunta duk mutum ko kungiyar da suka nemi tada zaune tsaye a jihar Kano ba. Hoto: Nigeria Police
Asali: Twitter

A ranar 17 ga watan Nuwamba, Kotun Daukaka Kara mai zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke na korar Yusuf, dan takarar jam'iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin addini da 'yan sanda suka gana da su

Tun a lokacin Yusuf da jam'iyyar NNPP suka garzaya Kotun Koli don shigar da sabuwar kara da ke kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Karar.

Da ya ke jawabi a ranar Alhmis a wani taron tattaunawa da kungiyoyin addini na Tijjaniya, Qadiriyya, Shi'a, Izala da kungiyar kirsta ta kasa, Gumel ya bukaci malaman su rinka yin wa'azi kan muhimmancin zaman lafiya a jihar.

"Ba zamu gaza wajen hukunta duk mutum ko kungiyar da suka nemi tada zaune tsaye a jihar Kano ba," kamar yadda NAN ta ruwaito Gumel yana cewa.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: NNPP ta bayyana matsayarta kan hukuncin Kotun Daukaka Kara, ta fadi matakin gaba

Ya ce:

"Za mu iya dakile duk wani yunkurin tada tarzoma idan har mazauna garin suka bamu hadin kai wajen kai rahoton duk wani abu da ba su gamsu da shi a muhallinsu ba.

Manufar ganawar 'yan sanda da malaman addini a Kano

Ya kuma bukaci malaman addinin da su guje biye wa mutane ko kungiyoyi musamman na siyasa wajen yin amfani da su don tayar da tarzoma, The Cable ta ruwaito.

"Kar ku yarda da wanda zai umurce ku da yin wa'azi da zai tayar da zaune tsaye musamman da ake shirin yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar a bikin kirsimeti da sabuwar shekara da ke zuwa."

Kwamishinan 'yan sandan ya kuma ce manufar taron shi ne rokon malaman addinin da su shawarci mabiyansu wajen ba da bayanan sirri ga 'yan sanda da zaran sun ga wani ko wasu na shirin tayar da tarzoma.

Yan sanda sun kama masu laifi 130, sun gurfanar da 61

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a shari'ar neman tsige gwamna mai ci, ta ba da dalilai

A wani labarin, kun karanta cewa rundunar 'yan sanda ta sanar da nasarar da dakarunta suka samu na afke masu laifi 130 a jihar Katsina

Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan fashi 38, masu kisan kai 16, da sauransu, kuma ta kubutar da mutum 69, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.