Harin Bam a Kaduna: Amurka Ta Ba Najeriya Shawarar Amfani da Fasahar AI Wajen Kai Farmaki
- Kasar Amurka ta shawarci Najeriya kan horas da dakarun sojinta wajen amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) yayin kai hare-hare
- Amurka ta kuma jajanta wa al'ummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, inda a karshen makon da ya gabata sojoji suka farmake su bisa kuskure
- Kasar ta ce yin amfani da fasahar AI zai kawo karshen kai wa fareren hula hari, kasancewar fasahar na iya bambance dan ta'adda da farar hula
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar tabbatar da lafiya da amfani da makamai ta Amurka ta ce yin amfani da fasarar Artificial Intelligence (AI) zai taimaka wa dakarun sojin Najeriya wajen kai farmaki.
A cewar hukumar, yin amfani da fasahar AI zai iya bambance farar hula da dan ta'adda wanda zai rage kai farmakin kuskure kan fararen hula.
Idan za a iya tunawa Legit Hausa ta ruwaito yadda dakarun soji suka kaddamar da harin bam a wani kauyen jihar Kaduna, a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, 2023, Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhimmancin amfani da fasahar AI wajen kai farmaki
Rundunar sojin ta bayyana cewa dakarunta sun samu kuskure ne wajen kai harin, sun saki bama-baman ne da tunanin akwai 'yan ta'adda a garin, sai ya fada kan masu maulidi a garin Tudun Biri, karamar hukumar Igabi, a jihar.
Vanguard ta rahoto mataimakin babban sakataren hukumar, Paul Dean na bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis.
Hukumar ta ce amfani da fasahar AI zai dakile rundunar soji daga karya dokokin da suka shafi dan Adam da kuma inganta hare-haren su kan 'yan ta'adda.
Ya ce:
"Da farko muna mika sakon ta'aziyya da jaje ga wadanda wannan iftila'i ya fada masu. Ina ga a wannan gabar ya kamata in yi magana kan muhimmancin amfani da fasahar AI.
"Ma damar sojojin Najeriya za su rinka amfani da fasahar AI wajen kai hare-hare, to za a kawo karshen farmakar fararen hula da gan-gan."
Amurka za ta taimakawa Najeriya kan amfani da makamai
Dean ya kuma ce Amurka na shirye don taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen kawo karshen lalacewa, ko kai hare-haren makamai ba bisa ka'ida ba.
Ya ce:
"Hukumar mu za ta taimaka wa Najeriya wajen bunkasa yaki da ta'addanci ta hanyar amfani da makamai ba tare da saba ka'idoji na 'yancin dan Adam ba.
"Haka zalika za mu taimakawa Najeriya a shirin ta na haramta amfani da makamai masu hatsari, daukar matakai na kai hare-haren sama ba tare da matsala ba, da dai sauransu."
Kamfanin Amurka ya dakatar da aiki a Najeriya
A wani labarin, kamfanin Amurka, mai sarrafa Pampers, Always, Oral B, Ariel, Ambi-pur, SafeGuard, Olay da Gillette ya sanar da daina aiki a Najeriya.
Kamfanin mai suna P&G ya yanke shawarar rufe kamfaninsa ne sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng