‘Yan Kasuwa Sun Koka Game da Asarar N13bn da Ake Yi a Mako Saboda Rufe Iyakoki
- Wasu ‘yan kasuwa da ke neman kudi a Arewacin Najeriya sun ce rufe iyakoki da aka yi ya kawo masu asara
- A kowane mako, manyan ‘yan kasuwar suna rasa biliyoyin kudin da ya kamata a ce ya shigo hannunsu
- Kungiyar ‘yan kasuwan sun roki gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Tinubu ta bude iyakoki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Wata kungiya ta ‘yan kasuwan Arewacin Najeriya ta koka cewa rufe iyakoki ya durkusar da hanyar neman kudin mutanenta.
Kungiyar Arewa Economic Forum ta roki gwamnatin tarayya ta nema masu wata hanyar kasuwanci, Leadership ta kawo rahoton.
A cewar ‘yan kasuwan, a kowane mako, suna yin asarar kusan N13bn a sakamakon rufe iyakokin kasar nan da gwamnatin tayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji su ka yi a Nijar, amma hakan bai hana ta koka a kan rufe iyakarta da Najeriya ba.
Shugaban wannan kungiya, Alhaji Ibrahim Danda-Kate ya ce ya kamata gwamnati ta fahimci tasirin wannan matakin da aka dauka.
Danda-Kate ya ce ta Nijar ake bi domin zuwa kasuwanci a kasashen Mauritania da Mali, a yanzu harkar kasuwanci ta tsaya cak.
Za ayi asarar kayan Daloli saboda rufe iyaka
Hamza Sale Jibia yake cewa akwai kwantenoni sama a 2000 na ‘yan kungiyarsu wadanda ke dauke da kayan da za su iya rubewa.
‘Dan kasuwar ya ce duk kwantena ta na cin dukiyar da ta kai $20,000 zuwa $50,000.
AFFPON ba ta jin dadin rufe iyakoki
Shugaban kungiyar AFFPON masu shigo da kaya daga ketare ya ce dukiyar da ake asara a mako ta kai akalla N13bn a dalilin tsarin.
Daily Trust ta rahoto Miftahu Ya’u yana rokon a bude iyakar Lolo da ta hana Najeriya da Benin, ya ce an rufe iyakar ya tsaida kasuwanci.
Alakar Najeriya da kasar Nijar
Hambarar da gwamnatin farar hula ya jawo Bola Tinubu ya umarci a rufe iyaka da Nijar mai makwabtaka da Sokoto, Kebbi da Jigawa.
Kamar yadda aka sani tun tuni, Jamhuriyyar Nijar ta kuma yi iyaka da jihohi irinsu Katsina, Borno da Yobe da ke Arewacin Najeriya.
Fatara ta tada tsohon bashi a Najeriya
Rahoton da aka samu ya nuna ‘yan majalisan 1992-1993 na Jamhuriyya ta uku sun ce akwai kudinsu da ba a biya su ba a shekarun baya.
Janar Sani Abacha ya raba ‘yan majalisar da kujerunsu da ya hambarar da gwamnatin farar hula da ya shiga ofis a karshen 1993.
Asali: Legit.ng