Kasafin Tinubu Ya Fusata Arewa, Ba a Ware Sisi Domin Aikin Wutan Mambilla a 2024 ba
- Shugaba Bola Tinubu bai ware sisin kobo da nufin biyan kamfanin da ke kwangilar Mambilla a 2024 ba
- Tun a shekarar 2017 gwamnatin Muhammadu Buhari ta amince a kashe $5.792bn domin wannan katafaren aiki
- Har yau dai maganar samar da 3000mw daga tashar ta Mambila ba tayi nisa ba bayan shekaru fiye da 40
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Babu abin da aka ware domin ayi aikin kwangilar wutan lantarkin Mambilla da ke garin Gembu a jihar Taraba a shekarar 2024.
Rahoton Daily Trust ya ce gwamnatin tarayya ba tayi la’akari da wannan gagarumin aiki wajen tsara kasafin kudin shekara mai zuwa ba.
Kudin da za a kashe a ma'aikatar lantarki
Abin ban mamakin shi ne kasafin kudin ya nuna ma’aikatar lantarki za ta kashe N400m domin shirya taro da za a ketare a shekarar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A 2024, ma’aikatar lantarki ta tarayya ta na shirin kashe N300m wajen jawo masu hannun jari da za su kawo kudi a harkar wuta a Najeriya.
Binciken da aka yi ya nuna a kasafin kudin na badi wanda ake sa ran zai kawo cigaba a kasar, an ware N96.8bn da sunan aikin DISREP
Masana za su ci N120bn wajen kokarin gano hanyoyin da za a bi wajen samun wuta sannan rushe-rushe da za ayi a shekarar za su ci N3.3bn.
Mambilla: Majalisa za ta kira Ministan wuta
Ganin haka ne jaridar ta ce kwamitin wuta na majalisar dattawa ta bukaci a gayyato Adebayo Adelabu wanda shi ne ministan harkar lantarki.
Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce a lokacin da aka gabatar da kasafin, sun ga an manta da aikin Mambilla, don haka dole ayi masu bayani.
"Arewa ake yaka a mulkin Tinubu" - NEF
Kungiyar manyan Arewa ta NEF ta zargi gwamnatin Bola Tinubu da watsi da Arewa.
Kakakin NEF na kasa, Abdul’azeez Suleiman ya shaida cewa kashe N400m wajen taro ya nuna gwamnati ba ta san menene mafi muhimmanci ba.
Manyan na Arewa sun ce kammala aikin zai taimaka wajen kawo cigaba da samar da sana’o’i 50, 000, amma ba a so a ga yankin ya samu cigaba.
Dabbobi za su ci N200m a kasafin Tinubu
Ana sa rai cewa har dabbobi za su samu sama da Naira miliyan 200 daga kasafin kudin shekarar 2024 kamar yadda bayanai su ka tabbatar.
Tafiye tafiyen Bola Tinubu da Kashim Shettima kuwa za su ci N16bn a shekarar 2024.
Asali: Legit.ng