Bola Tinubu da Kashim Shettima Za Su Kashe Naira Biliyan 15 a Tafiye Tafiye a Shekara 1
- Fadar shugaban kasa ta samu kason biliyoyi daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 da gwamnatin tarayya ta yi
- Abin da aka ware da sunan tafiye-tafiyen Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a shekarar badi ya zarce N15bn
- Shugabannin Najeriya za su iya batar da sama da N600m kan kayan abinci, sannan za a saye motocin N6bn a 2024
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima da hadimansa za su kashe N15.961bn a wajen tafiye-tafiye a shekara mai zuwa.
Vanguard ta ce an samu wadannan bayanai ne daga kasafin kudin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gabatar gaban majalisar tarayya.

Asali: Facebook
Yawon Tinubu, Shettima zai ci N16bn
Bola Ahmed Tinubu da mukarrabansa za su batar da N7.630bn da sunan tafiye-tafiye a cikin gida da zuwa kasashen ketare a shekarar badi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan 'yan majalisa sun amince da kasafin kudin yadda aka gabatar da shi, mataimakin shugaban kasa zai ci N6.902bn a zirga-zirga.
Kasafin kudin na 2024 ya nuna tafiye-tafiyen da shugaban kasan da mataimakinsa za su yi a cikin Najeriya za su lashe N638.5m da N618.39m.
An ware wasu N6.484bn saboda tafiye-tafiyen jami’an da ke cikin fadar Aso Rock yayin da aka samu rahoto har dabbobi za su samu N201m.
A shekara mai zuwa, The Nation ta ce fadar shugaban kasa za ta kashe N40.61bn wajen ayyuka da biyan albashin ma’aikata da sauransu.
Gina ofisoshi da gyare-gyare a Aso Rock
Gyare-gyaren wuta da sauran abubuwa da za ayi za su ci N9bn a fadar shugaban kasar, wani fitaccen kamfanin kasar waje ake ba aikin.
Abin da aka ware domin gina ofisoshin masu ba shugaban kasa da mataimakinsa shawara shi ne N3bn a lokacin da ake kukan rashin kudi.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba na Kano zai faranta ran tsofaffin ma’aikata, an tsaida ranar fara biyan kudin giratuti
Za kuma a kashe wasu N3bn a saye da gyaran kayan aikin fadar shugaban kasa.
Motoci da abincin Tinubu za su ci N11bn
Motoci kurum za su ci N6bn a fadar shugaban kasa kamar yadda aka yi lissafin cewa Tinubu da mataimakinsa za su ci abinci na N5.128bn.
A cikin wannan N5.128bn, za a biya kudin taro da shakatawa da sayen manhajojin komfuta, gyare-gyaren komfutocin za su ci N980m.
Tinubu ya dawo da kwangilar INTEL
Da aka soke kwangilar da aka ba INTEL, an samu labari cewa hakan ya jawo asarar N120bn a cikin 'yan shekaru ga gwamnatin tarayya.
Da gwamnati ta ji uwar-bari, an kira kamfanin ya cigaba da aiki a tasoshin ruwan Najeriya bayan Atiku Abubakar ya saida hannun jarinsa.
Asali: Legit.ng