Inalillahi wa'inna'ilaihi Raj'iun : Allah ya yi wa mai martaba sarkin Katagum Rasuwa a ranar Asabar

Inalillahi wa'inna'ilaihi Raj'iun : Allah ya yi wa mai martaba sarkin Katagum Rasuwa a ranar Asabar

- Sarkin Katagum ya rasu bayan ya jinya na tsawon shekaru 5

- Yakubu Dogara ya jajanta ma mutanen Bauchi akan babban rashin da suka yi

- Za a yi jana'izar mai martaba Alhaji Mohammed Kabir Umar a safiyar ranar Lahadi

Allah yayi wa mai martaba sarkin Kataguma, Alhaji Mohammed Kabir Umar, rasuwa a ranar Asabar 11 ga watan Disamba 2017.

Marigayi mai martaba Alhaji Mohammed Kabir Umar, yayi jinya na tsawon shekaru biyar kafin kafin Allah ya karbi rayuwan sa.

Legit.ng ta samu rahoton cewa za ayi janaizar sa a safiyar yau Lahadi da misalin karfe 11.am a garin Azare.

Inalillahi wa'inna'ilaihi Raj'iun : Allah ya yi wa mai martaba sarkin Katagum Rasuwa a ranar Asabar
Inalillahi wa'inna'ilaihi Raj'iun : Allah ya yi wa mai martaba sarkin Katagum Rasuwa a ranar Asabar

Kakakin majalissar datawa Yakubu Dogara, yace mutuwar mai martaba sarkin Katagum Alhaji Mohammed Kabir babban rashi ne ga alummar Bauchi.

KU KARANTA : Babu abin da ke sosa mani rai kamar in ga yara sun fito gani na – Inji Buhari

Dogara ya bayyana haka ne ta mai magana da yawun bakkin sa Turaki Hassan, a lokacin da yake mika ta’aziyar sa ga iyalan marigayi.

Ana sa ran gwaman jihar Bauchi Mohammed Abubakar, sarakunan Arewa da manyan yan siyasa za su halarci janaizar Alhaji Mohammed Kabir.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng