Farin Ciki Yayin Da Gwamnan PDP Ya Sanar Da Ranar Biyan Albashin Watan 13

Farin Ciki Yayin Da Gwamnan PDP Ya Sanar Da Ranar Biyan Albashin Watan 13

  • Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya amince da ranar Laraba 27 ga watan Disamba domin biyan ma’aikata albashin wata na 13 a jihar
  • Kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar, Chris Nehikhare ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 5 ga watan Disamba
  • Nehikhare ya ce Gwamna Obaseki ya cigaba da ba da fifiko ga jin dadin ma’aikatan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Birnin Benin, jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya amince da ranar biyan albashin watan 13 ga ma’aikata a jihar.

Chris Nehikhare, kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Tinubu ya fara biyan albashin ma'aikata da aka rike

Obaseki zai biya albashin watan 13
Gwamna Obaseki zai biya ma'aikatan Edo albashin watan 13 Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Kwamishinan ya ce Obaseki ya cigaba da ba da fifiko ga jindaɗin ma’aikata a jihar, kuma zai cigaba da cika alkawarin da ya ɗauka na samar da ingantaccen yanayin aiki mai kyau ga ma'aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan Edo za su ƙarbi albashin wata 13

Gwamnatin dai za ta biya albashin watan Disamba a ranar Litinin 11 ga watan Disamba, yayin da ma’aikata za su samu albashin watan 13 a ranar Laraba 27 ga watan Disamba.

Jam’iyyar PDP mai cike da farin ciki, ta bayyana hakan ta shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Sanarwar ta gwamnatin Edo tana cewa:

"Gwamna Godwin Obaseki, ya amince da ranar biyan albashin ma’aikata na watan 13. Za a biya albashin watan Disamba a ranar 11 ga Disamba yayin da albashin watan 13 za a biya a ranar 27 ga Disamba.

Kara karanta wannan

Kwanaki kadan kafin barin kujerar mulki, gwamnan APC ya kirkiri sabuwar ma'aikata, ya fadi dalili

"Wannan ya yi daidai da jajircewar da Gwamnan ya yi wajen kyautata jindaɗin ma’aikata a jihar, wanda aka dade ana yi tsawon shekaru bakwai. Ya dace a ce gwamnatin Gwamna Obaseki ba ta yi wasa da biyan albashi ba."
"A wannan lokaci, ba a yi ƙasa a gwiwa ba, domin ma’aikata suna karbar albashinsu a ranar 26 ga wata ko kafin ranar 26 ga wata, haka ma ƴan fansho a jihar."

Obaseki Ya Magantu Kan Takarar Shaibu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi magana kan takarar gwamnan da mataimakinsa Philip Shaibu ya fito.

Obaseki ya ce mambobin PDP ne kaɗai za su yanke ko Shuaibu zai zama dan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng