Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Yi Martani Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ya Aike da Saƙo Ga Tinubu

Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Yi Martani Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ya Aike da Saƙo Ga Tinubu

  • Sheikh Ɗahiru Bauchi ya buƙaci Bola Ahmed Tinubu ya tabbata an hukunta sojojin da suka kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna
  • Fitaccen Malamin ya aike da saƙon ta'aziyya ga al'ummar Musulman Najeriya da na duniya kan wannan ibtila'i da ya ci rayuka
  • Ya ce abin da ɗaure kai sojojin sama sun nesanta kansu da harin amma sojin kasa sun ce su suka yi kuskuren

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya yi martani kan harin sojojin da ya halaka masu bikin Maulidi a Kaduna.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Kaduna: A hukunta duk mai hannu a kisan masu Maulidi, Sheikh Ɗahiru Bauchi Ga Tinubu Hoto: Dahiru Bauchi
Asali: UGC

Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbata an hukunta duk mai hannu a kisan Musulmai a taron Maulidi a ƙauyen Tudun Biri.

Kara karanta wannan

Wakilan Gwamnatin Kaduna sun dira garin da sojoji Suka kashe bayin Allah a taron Maulidi

Sama da mutum 90 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin bam ɗin sojijin kasa, wanda rundunar ta ce kuskure ne, ba da gangan ta yi ba, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shahararren malamin ya kuma roƙi gwamnati ta gaggauta toshe duk wata kafa domin dakile yiwuwar tashin rikici da tsare rayuka da mutuncin yan Najeriya.

Shehin malamin ya aike da saƙon ta'aziyya

Ɗahiru Bauchi ya kuma jajantawa iyalan mamatan da daukacin al’ummar musulmi, kana ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu, ya kuma saka musu da gidan Aljanna.

Ya ce shi da mabiyansa suna cikin bakin ciki kuma sun kasa fahimtar dalilin da ya sa wasu ke kashe musulmai da ba su da hannu a tayar da hargitsi ko rashin zaman lafiya.

Shehin Malamin ya ce:

"Muna son gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta shiga tsakani, ta tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu a harin Mauludi, kuma a hukunta sojojin da suka aikta laifin."

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

"Muna cikin yanayin ruɗani, su kuma shugabanni sun rufe idonsu kan waɗanda ake zalunta, waye mai lafi? Gwamnati ko wani daban? Bai kamata a yi wasa da koken mutane ba."
"Muna jaddada bukatar mahukunta su gudanar da cikakken bincike kan wannan bala'i da ya yi ajalin mutane da yawa. A binciko yadda aka yi jirgin ya saki bam a taron Maulidi, sojojin sama sun ce ba ruwansu, na ƙasa sun ce su suka yi."

Gwamnatin Kaduna ta tura wakilai kauyen Tudun Biri

A wani rahoton kuma wakilan gwamnatin Kaduna karkashin mataimakiyar gwamna sun kai ziyarar ta'aziyya kauyen Tudun Biri ranar Talata.

Wannan ya biyo bayan umarnin Gwamna Uba Sani na gudanar da binciki kan harin sojojin da ya kashe bayin Allah a kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel