Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata

Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata

  • Wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace sojan da aka kama da laifin kisan Sheikh Aisami, an sauya masa wurin aiki ne bayan yayi wa kwamandansa sata
  • Duk da kwamandan ya kasa fitar da kwakwarar shaida kan cewa Gabriel ne ya sace masa N480,000, yayi tsinuwa tare da cewa in halinsa ne dubunsa zata ciki
  • A watan Yulin da ya gabata lamarin ya faru, a watan Augusta aka kama Gabriel da laifin halaka Sheikh Aisami tare da yunkurin tserewa da motarsa

Yobe - Sojan da aka kama kan zargin halaka fitaccen malamin addinin Islama a jihar Yobe, Goni Aisami, an sauya masa wurin aiki ne sakamakon sace N480,000 da yayi wa kwamandansa.

Sojan mai suna John Gabriel, mai mukamin Lance Corporal, yana aikin sojan ne da bataliya da 241 Recce dake Nguru, kuma an kama shi ne matsayin wanda ake zargi da sace N80,000 da N400,000 a lokuta daban-daban kafin a mayar da shi kan titi, wata majiyar sojoji tace.

Kara karanta wannan

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

Nigerian Army
Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sojan shi ne dogarin kwamandan bataliyar, GS Oyemole, mai mukamin kanal kafin a sauya masa wurin aiki a watan Yuli saboda muguwar dabi'arsa, majiyar da ta sanar da Premium Times ta tabbatar.

“Kwamandan shi dole yasa aka sauya masa wurin aiki saboda ya kasa fitar da shaidar da zata tabbatar cewa shi ya sata kudin amma yayi tsinuwa kuma ya sanar da cewa idan har halinsa ne, zai ga karshensa," ya kara da cewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Abun mamaki, ranar da kwamandansa, Oyemole ya mikasa ga sabon kwamanda, aka kama Gabriel da zargin kashe malamin addinin Islaman," majiyar tace.

Ya kashe malamin da bindigar da yake da ita a boye cikin gadon sojojin da ya nado bayan malamin ya rage masa hanya zuwa garin Jaji Maji dake karamar hukumar Karasuwa ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, yace Gabriel na hannun 'yan sanda tare da dayan wanda ake zarginsu tare mai suna Adamu Gideon.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Biliyoyin da Ake ci Duk rana a Tallafin Man Fetur

An cafke sojojin ne da ake zarginsu da zama masu laifi. Majiyoyi sun ce sun kashe malamin ne bayan sun ga alamun kudi a motarsa yayin da yake dawowa daga Kano.

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

A wani labari na daban, an kara samun bayanai kan mutuwar Sheikh Goni Aisami, fitaccen malamin addinin Islama na Yobe jihar Yobe wanda aka bindige a ranar Juma'a.

Kamar yadda DSP Dungus Abdulkarim, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe ya bayyana, mutum biyun da ake zargi sojoji ne daga bataliya ta 241 sake Recce a Nguru sun shiga hannu.

Daily Trust ta rahoto cewa, yace lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan Aisami ya ragewa daya daga cikin wadanda ake zargin hanya.

Kakakin rundunar 'yan sandan yace Aisami na tuka motar daga Gashua zuwa Nguru, lokacin da wanda aka zargin ya tsayar da shi da kayan gida dauke da gado kuma ya roki malamin da ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Hotunan yadda aka kori jami'in sojin ruwan Najeriya daga aiki saboda aikata luwadi

Asali: Legit.ng

Online view pixel