Harin Bam a Kaduna: Mun Yi Takaici, Shugaban Sojoji Ya Roki Afuwa Kan Kisan Mutum 85

Harin Bam a Kaduna: Mun Yi Takaici, Shugaban Sojoji Ya Roki Afuwa Kan Kisan Mutum 85

  • Rundunar sojojin Najeriya ta nemi yafiyar al'ummar Tudun Biri, gwamnatin Kaduna da al'ummar jihar bisa harin bam na ranar Lahadi da ta gabata
  • Shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Lagbaja ya nemi yafiyar yayin da ya ziyarci jihar Kaduna don gani da ido kan iftila'in da ya faru
  • Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin soji ya saki bama-bamai a kan wasu masu maulidi a Kaduna, wanda ya yi silar mutuwar mutane 85

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Shugaban sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana mummunan harin da ya hallaka mutane 85 a jihar Kaduna a matsayin abin takaici.

Lagbaja wanda ya ziyarci jihar Kaduna a ranar Talata, ya ce hakan ba za ta sake faruwa a hukumar sojin kasar karkashin kulawarsa ba.

Kara karanta wannan

Izala ta yi Allah wadai da kisan masu bikin Maulidi a Kaduna, ta tura sako

Rundunar soji ta nemi afuwar al'ummar Kaduna kan kisan mutum 85
Shugaban sojojin Najeriya ya nemi afuwar hakimi, al'ummar garin Tudun Biri, gwamnatin Kaduna da ma al'ummar jihar kan harim bam da ya yi ajalin mutum 85. Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Shugaban sojojin ya ziyarci garin Tudun Biri, inda waki'ar ta faru tare da tattaunawa da mutanen garin. Ya kuma ziyarci asibiti don duba wadanda suka jikkata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan zai taimaka mun na kara fahimtar irin barnar da aka yi don kara mun kaimi wajen zurfafa bincike don ganin bakin zaren yadda lamarin ya faru."

A cewar Lagbaja.

Shugaban sojojin kasan ya samu wakilacin manyan jami'ai a rundunar soji da kuma babban janar da ke jagorantar rundunar soji ta farko, Channels TV ta ruwaito.

Rundunar soji ta roki yafiya

Tawagar ta kuma ziyarci Dangaladiman Zazzau, hakimin Rigasa, Architect Aminu Idris, da wasu shugabannin yankin da abin ya shafa.

Laftanal Janar Lagbaja ya bayyana cewa ya ziyarci Tudun Biri don gane wa idonsa barnar da aka yi, tare da jajanta masu da kuma neman yafiyarsu a madadin rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

Ya ce suna neman afuwar hakimi, al'ummar garin da kuma gwamnatin jihar Kaduna da ma al'ummar jihar baki daya kan wannan lamari, rahoton The Sun.

Lagbaja ya ce ya bayar da umurnin gudanar da babban bincike don gano yadda hakan ta faru da kuma gano inda aka yi kuskure da ya kai ga wannan iftila'in.

An saka jirgin shugaban Najeriya a kasuwa, ana neman mai saye

A wani labarin na daban, rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta sanya jirginta na Falcon 900B a kasuwa kan dalar Amurka, inda take neman mutane su taya.

NAF ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ce ta amince da sayar da jirgin kirar Falcon 900B, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.