Kamar Almara: Matar Aure Ta Datse Igiyar Aurenta Na Wata 6, Bidiyon Ya Jawo Muhawara

Kamar Almara: Matar Aure Ta Datse Igiyar Aurenta Na Wata 6, Bidiyon Ya Jawo Muhawara

  • Wata mata ta wallafa a shafinta na TikTok dalilin da ya sa ta yanke shawarar datse igiyar aurenta duk da bai wuce wata shida ba
  • Matar wacce ba a gano asalin sunanta ba, ta ce ta gaji da fadace-fadacen mijin, inda ta nemi kawarta tazo ta raba ta da gidan
  • Bidiyon ya jawo cece kuce a kafar, inda wasu ke yin kalaman karfafa mata guiwa, wasu kuma na magana kan rashin karkon auren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wasu lokutan aure na zuwa da nashi matsalolin la'akari da cewa zama ne na mutane biyu, kuma kowannensu na da ra'ayin da ya saba wa na dayan.

Wata mata a Tiktok @makungothulani, ta jawo muhawara a kafar bayan wallafa bidiyonta tana kokarin datse igiyar aurenta na watanni shida.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan matar da ta lakadawa mijinta duka saboda yana hira da yan mata

Matar aure ta kawo karshen aurenta na wata 6
Wata mata ta gaza jure ci gaba da zaman aurenta mai cike da tashin hankali. Hoto: Grace Cary/Getty Images, @makungothulani/TikTok
Asali: UGC

A cikin bidiyon, an ga matar wacce har yanzu ba a gano ko ita wacece ba, tana tattara kayanta tare da cire zoben aurenta daga yatsanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce ta gaji da cacar baki da fadan da suke yi da mijin, inda ta nemi kawarta tazo ta dauke ta daga gidan auren nata, Legit ta ruwaito.

Kalli bidiyon a kasa:

Kotu ta daure matar da ta lakadawa mijinta duka a Kano

A wani labarin, kotun majistire da ke Rijiyar Lemu, jihar Kano, ta bayar da ajiyar wata mata, Hafsa Ibrahim a gidan gyara hali kan lakadawa mijinta Jamilu Muhammad duka.

Matar ta lakadawa mijinta duka ne da wayar dutsen guga, tare da kekketa masa suturarsa har kala casa'in kan zargin yana hira da 'yan mata a wayarsa, Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Yawan kuri'u ba shi ne kadai alamar nasara a zabe ba, cewar Doguwa

Hafsa ta karyata zargin ta duki mijinta Jamilu

Mai shigar da kara, Usman Shuaibu Dala, ya shaida wa kotun cewa Hafsa ta ji wa mijinta rauni bayan dukansa a kai da dutsen guga, Daily Trust ta ruwaito.

"Duk da haka matar ba ta hakura ba, sai da ta sanya almakashi ta yanka kala casa'in na suturar mijin tare da kwace masa wayarsa da ta kai naira dubu tamanin."

A cewar mai gabatar da karar.

Sai dai, Hafsat ta karyata wannan zargi da ake yi mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel