Yanzu Yanzu: Yusuf Bichi ya kama aiki a matsayin shugaban DSS
Yusuf Magaji Bichi, sabon shugaban hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ya kama aiki a yau a hedkwatar hukumar domin tafiyar da shugabancin hukumar tsaron.
Peter Afunanya, kakakin hukumar yace Bichi yayi jawabi ga ma’aikatan sannan ya nemi goyon bayan mambobin.
Ya sha alwashin yin aiki tare da su a matsayin tawaga guda. Yace manufarsa shine yin aiki yadda ya kamata domin inganta hukumar DSS da kuma tabbatar da jin dadin ma’aikatan hukumar.
Bichi ya kuma ba da tabbacin cewa zasu ba gwamnati cikakken goyon baya wajen sake gina tattalin arziki, tabbatar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
KU KARANTA KUMA: Sarkin Ogoni ya nada wa Shugaba Buhari sarauta
Ya kuma bukaci ma’aikatan da su gudanar da aiki akan wannan tafarki. Ya kuma bukaci da su mutunta doka tare da daraja yancin dan Adam.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta-janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS).
Sabon shugaban zai karbi aiki daga hannun Matthew Seiyeifa, wanda yam aye gurbin Lawal Daura da aka dakatar.
Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ne ya bayar da sanarwar a wani jawabi da ya saki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng