Gwamnan Jihar Kwara Ya Samu Nasarar Zama Sabon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Gwamnan Jihar Kwara Ya Samu Nasarar Zama Sabon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya

  • Ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta zaɓi gwamnan jihar Kwara na jam'iyyar APC, a matsayin sabon shugabanta
  • Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya maye gurbin gwamna Aminu Waziri Tambuwar, mai barin gado na jihar Sokoto
  • Ƙungiyar gwamnonin ta kuma zaɓi, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin mataimakin shugabanta

Abuja - Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF).

Ya maye gurbin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda wa'adin mulkinsa ya ke ƙarewa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Gwamnan jihar Kwara ya zama sabon shugaban NGF
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq Hoto: Intelregion.com
Asali: UGC

Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da Tambuwal ya rattaɓawa hannu a ƙarshen zaman gaggawa da gwamnonin suka yi a ranar Talata da daddare, a birnin tarayya Abuja, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

A cewar takardar, Abdulrazaq ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin ba tare da wata jayayya ba, yayin da aka zaɓi gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ɓangare na takardar na cewa:

"A dangane da shugabancin wannan ƙungiyar, gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya samu nasarar zama shugaba ba tare da jayayya ba, sannan gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zama mataimakinsa."

Jaridar Vanguard tace kakakin watsa labarai na gwamnan Rafiu Ajakaye, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ga manema labarai, a safiyar ranar Laraba a birnin Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Gwamnan ya sha alwashin yin aiki tuƙuru

Gwamnan ya sha alwashin ci gaba da tafiya kan turbar da ƙungiyar ta ke a kai, ta samar da ci gaba da haɗin kai a tsakanin gwamnonin ƙasar nan, domin ciyar da ƙasar nan gaba.

Abdulrazaq ya nuna godiyarsa ga takwarorinsa kan wannan amana da suka ba shi, inda ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta cigaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da shugaban ƙasa, majalisar tarayya da dukkanin wasu hukumomi da suka dace.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa

A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Gombe, ya samu nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya (NGSF).

Gwamna Inuwa Yahaya ya gaji gwamnan jihar Plateau mai barin gado, Simon Lalong a shugabancin ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel