Gwamnatin Jihar Kwara Za Ta Yi Jigilar Mayar da Dalibai Zuwa Makarantunsu Kyauta

Gwamnatin Jihar Kwara Za Ta Yi Jigilar Mayar da Dalibai Zuwa Makarantunsu Kyauta

  • Gwamnatin jihar Kwara ta shirya tallafawa daliban da za su koma makaranta a mako mai zuwa
  • Kungiyar malaman jami'a sun janye yajin aiki, dalibai a fadin Najeriya na ci gaba da shirin komawa makaranta
  • An shafe watanni akalla takwasi daliban Najeriya na zaman gida, gwamnatin Kwara za ta mai da dalibai makaranta kyauta

Jihar Kwara - Domin rage radadi ga dalibai, gwamnatin jihar Kwara za ta yi jigilar daliban jihar zuwa jihohin ketare da suke karatu a fadin Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta yanje yajin aikin watanni takwas da ta yi tun watan Fabrairun bana.

Jihar Kwara ta shirya tallafawa daliban da za su koma makaranta a makon nan
Gwamnatin Jihar Kwara Za Ta Yi Jigilar Mayar da Dalibai Zuwa Makarantunsu Kyauta | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamishinan manyan makarantun jihar, Dr Alabi Abolore ne ya bayyana manufar gwamnati na jigilar dalibai kyauta a jiya Litinin 24 ga watan Oktoba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dangote Ya Yi Alkawarin Aiki Ga Duk Dalibin Jami'ar KUST Da Ya Samu 1st Class Da 2-One

A cewar sanarwar da sakatariyar yada labarai ta jihar, Mansurat Amuda-Kannike ta fitar, ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnatin Mallam AbdulRahman AbdulRazak na kara yalwar raba romon dimokradiyya ga daliban manyan makarantu 'yan Kwara a fadin kasar nan."

Yadda za a tallafawa daliban

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, daliban da za su koma makaranta a yankin Arewacin Najeriya dole su taru a ranar Asabar 29 ga wata da misalin karfe 6:30 na safe don bincikarsu a ma'aikatar ilimi ta jihar dake hanyar Offa a GRA.

Hakazalika, kwamishinan ya ce, ma'aikatar ilimi za ta kuma fara shirye-shiryen sakin kudin tallafi da zarar an bude sahar rajistar yanar gizo, rahoton Daily Sun.

Daga karshe ya mika godiya ya iyaye da dalibai bisa ciyar da jihar Kwara gaba da kuma ba gwamnatin jihar goyon baya.

Zan Yi Kamfen da Lambar Yabon da Shugaba Buhari Ya Bani, Inji Gwamnan PDP Wike

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kasar Dubai Ta Dakatad Da Baiwa Yan Najeriya Biza Gaba Daya

A wani labarin na daban, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa, zai yi amfani da lambar yabon da shugaban kasa Muhammadu ya bashi wajen yakin neman zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Wike ya bayyana hakan ne a wani taron nuna lambar yabon da Buhari ya bashi, wanda aka gudanar a babban birnin jiharsa, Fatakwal a daren jiya Litinin 24 ga watan Oktoba.

Yayin da yake sadaukar da lambar yabon ga ubangiji, ya kuma shaida cewa, gwamnatinsa ta samu nasarar yin ayyukan more rayuwa ne saboda kwarin gwiwar da yake samu daga mutanen jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel