Jami'ar Ahmadu Bello za ta gina matatan man fetur a yankin Neja Delta

Jami'ar Ahmadu Bello za ta gina matatan man fetur a yankin Neja Delta

Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria (ABU) ta fara gudanar da ayyukan gina matattan man fetur na zamani ta hanyar amfani da kayayakin gida Najeriya a yankin Neja Delta.

Jagoran aikin gina matatan man fetur din, Farfesa Ibrahim Mohammad-Dabo ne ya shaida wa manema labarai a wata hira da yayi da kamfanin dillancin na kasa (NAN) a garin Zaria da ke Kaduna.

A cewar Mohammed-Dabo wanda Farfesa ne kuma injiniya a sashen nazarin sinadarai, burin su shine su gina matattan man fetur na zamani wanda za'a rika amfani dashi wajen tace man fetur a kasar nan ba don rage dogaro da tacewa a kasashen waje.

Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria za ta gina matatan mai a yankin Neja Delta
Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria za ta gina matatan mai a yankin Neja Delta

DUBA WANNAN: Babu wani mahalukin da ya isa hana ni tsayawa takarar gwamna - Mataimakin gwamna Rochas

"Muna fata idan aka tallafa mana da isasun kudade, zamu kamalla wanda muke aiki a akai kuma zamu gina wasu matatun man fetir din a yankin Neja Delta tunda a nan ne akafi hakar man fetir din," inji shi.

Ya kuma kara da cewa aikin na bukatar kudi naira 18 miliyan amma duka amma naira 1.8 miliyan kawai aka ba su sai dai hakan bai sa sun karaya ba. Sunyi amfani da wannan kudin wurin tsare-tsare da kuma kera wasu daga cikin kayayakin aikin da suke bukata.

"Akwai lokutan da har kudin aljihun mu muke amfani dashi wajen aikin. Bayan mun kafa wadansu kayayakin aikin, mun gayyaci mahukuntar jami'ar kuma sunyi matukar farin ciki da aikin namu.

"Hakan ya sa Shugaban jami'an na wancan lokacin ya yi alkawarin tallafawa aikin namu ta hanyar samar mana da filaye, ruwa, lantarki da kuma tsaro," inji Mohammed-Dabo.

A takaice da jami'ar na taimaka musu da duka abin da suke bukata wajen ganin an kammala aikin cikin nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164