Nasarawa da Kuros Ribas Sun Tashi da Cinyoyi da Aka Rabawa Jihohi Biliyoyin Kudi
- Bankin duniya ya ba NG-CARES gudumuwa domin tallafawa wadanda annobar COVID-19 ta durkusa hanyar neman kudinsu
- Gwamnatin tarayya ta rabawa jihohin Najeriya da birnin tarayya Abuja tallafin Naira biliyan 135 a karkashin tsarin NG-CARES
- Dr. Abdulkarim Obaje ya ce akwai ka’idar da aka bi wajen bada tallafin, wannan ne ya sa jihar Nasarawa ta zo ta farko a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta raba N135.4bn ga jihohi da kuma birnin Abuja domin farfado da tattalin arziki bayan annobar COVID-19.
Rahoton da aka samu daga Punch ya nuna an raba kudin ne bayan lura da yadda jihohi su ka yi kokarin tada komadan tattalin arzikinsu.
NG-CARES ya ba jihohi tallafin N135bn
Shugaban tsarin NG-CARES, Dr. Abdulkarim Obaje, ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar ta bakin Mr. Suleiman Odapu a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suleiman Odapu shi ne jami’in yada labarai da sanarwa a karkashin tsarin na NG-CARES.
Bankin duniya ya tallafawa tsarin NG-CARES da $750m da nufin taimakawa kananan ‘yan kasuwa da manoman da COVID-19 ta taba.
Dr. Abdulkarim Obaje ya ce kudin da aka rabawa jihohin ya danganta ne da kokarin da su ka yi wajen taimakawa wadanda annobar ta shafa.
Dr. Obaje ya bayyana jihohin da su ka fi yin kokari da kuma adadin kudin da aka ba su.
Yadda aka yi rabon kudin tallafin
Jaridar ta ce jihar Nasarawa ce a kan gaba da ta samu N13.6bn, sai Kuros Riba mai N10.9bn sai kuma jihar Zamfara wanda ta tashi da N10.2bn.
Wadannan jihohi uku sun tashi da 34,873,631,583.62 daga cikin tallafin biliyoyin da aka raba, ma’ana su kadai sun samu fiye da 25% na kason.
Kokarin Gwamnatin Tinubu a Najeriya
Jawabin ya kara da cewa wannan wata nasara ce da aka samu a gwamnatin Bola Tinubu.
Sabon shugaban na Najeriya ya ci burin rage jarabar talaucin da ake fama da shi a Najeriya, wannan ya na cikin kudirorin gwamnatinsa.
An fara biyan giratuti a jihar Kano
Sabon Gwamnan jihar Kano ya tabbatarwa tsofaffin ma’aikata shi mai kaunarsu ne inda aka ji zai kashe N6bn wajen biyan giratutinsu.
Bayan shekaru 'yan fansho su na jiran hakkokinsu, Abba Kabir Yusuf ya share masu hawaye a Kano kamar yadda ya dauki masu alkawari.
Asali: Legit.ng