Bani da Katabus: Wanda Ya Kone Takardar Digirinsa Ya Yi Bayanin Dalilansa Na Bankawa Takardunsa Wuta
- Alvin Ilenre, dan Najeriya mai digiri a fannin Tarihi da Nazarin Duniya daga Jami’ar Ajayi Crowther, Oyo, yana fama da rashin aikin yi tun watan Fabrairun 2022.
- Bidiyon da ke nuna Ilenrena kona takaddunsa ya haifar da cece-kuce, wanda ya kai ga wannan tattaunawar da aka yi dashi kwanan nan inda ya bayyana dalilansa masu karfi
- Ba sabon abu bane a Najeriya dalibai su kammala digiri su kare babu aikin yi a gwamnatin ko kamfani saboda dalibai
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Edo - A wani yunkuri na neman sauki, Alvin Ilenre, dan Najeriya mai digiri dan asalin jihar Edo, ya kona takardar digirinsa, inda ya dasawa ‘yan kasar ayar tambaya kan dalilin da ya sa ya aikata wannan danyen aikin.
Da yake tattaunawa da jaridar Punch, a wata hira da aka buga a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, Alvin, wanda ya karanci tarihi da nazarin kasa da kasa a jami’ar Ajayi Crowther, jihar Oyo, ya ce bai da katabus tun watan Fabrairun 2022.
Rashin aiki yasa na kone digiri na – mai digiri a Najeriya
Ya ce babu abin da yake yi tun barinsa jami’a face buga-buga ta yau da kullum wanda yace ya gaji da zaman banza ba aikin ofis ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana kan babban dalilinsa na kona wasu takardunsa, kamar yadda aka gani a wani faifan bidiyo, Alvin ya ce yana bukatar sassautawa kansa ne, kuma takardun digirin nasa ba su da wani amfani a gare shi.
Ya ce kamar haka:
"Na kona su ne saboda wasu abubuwa da nake fama da su kuma ina bukatar in hutar da kainaa, shi ya sa na kona su."
Wasu takardu ya kone?
Da aka tambaye shi wadanne takardun ya kona, Alvin ya ce:
“Ban san inda na adana takardar shaidar kammala sakandare na a cikin wadannan duka ba, amma takardun da na kona su ne na jami’a da na firamare, da kuma na bautar kasa.”
Sai dai, ya ce duk da haka akwai wasu takardun da bai kone ba, bai kone takardun da ke da alaka da horon da ya samu na addini ba.
Zan siyar da digiri na, inji dan Najeriya
A wani labarin, wata budurwa ta fitar da kwalin digirinta don siyarwa a kafar sada zumuntar zamani saboda tsananin fusata don ta ce bashi da amfani.
Budurwar ta sanar da cewa za ta siyar da digirinta ne don ta gano bashi da amfani sakamakon rashin samun aikin da tayi da shi.
Baudurwar ‘yar kasar Afirka ta kudun ta fito da kwalin digirin ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu tare da tambayar mutanen da ta sani ko zasu siya. Idan kuwa akwai mai bukata, toh ya zo su sasanta don ciniki mai kyau.
Asali: Legit.ng