Zan sayar da takardun digiri dina ne, saboda na gano basu da wani amfani a rayuwata - Cewar budurwa

Zan sayar da takardun digiri dina ne, saboda na gano basu da wani amfani a rayuwata - Cewar budurwa

- Wata fusatacciyar budurwa ta wallafa tallar siyar da kwalin digirinta da za ta yi a kafar sada zumunta

- Ta bayyana cewa digirin nata bai yi mata wani amfani ba don haka idan da mai so ya garzayo don siyarwa za ta yi

- Tuni kuwa mutane da yawa suka fara tururuwar tsokaci a kan hakan tare da goyon bayanta, don a cewarsu nasu yana nan baya amfanin komai

Wata budurwa ta fitar da kwalin digirinta don siyarwa a kafar sada zumuntar zamani saboda tsananin fusata don ta ce bashi da amfani.

Budurwar ta sanar da cewa za ta siyar da digirinta ne don ta gano bashi da amfani sakamakon rashin samun aikin da tayi da shi.

Baudurwar ‘yar kasar Afirka ta kudun ta fito da kwalin digirin ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu tare da tambayar mutanen da ta sani ko zasu siya. Idan kuwa akwai mai bukata, toh ya zo su sasanta don ciniki mai kyau.

Ai kuwa babu dadewa ta fara samun martani daga jama’a da yawa. Kamar yadda budurwa ta ce gara ta fara aikin taimako a yankinta, sai wani ya ce mata ai aikin taimako dama ba don gwamnati ake yin shi ba. A kan duba abinda yanki ke bukata ne sai a yi musu.

KU KARANTA: Ku daina jiran masu arziki, ku auri wanda ya samu kuyi arzikin tare - Anita Joseph ta shawarci 'yan mata

Wani kuwa ya kara da karfafa mata guiwa ne inda ya ce shi ma kuwa haka yake ji tamkar ya kona kwalin digirinshi. Don har yanzu bai ga tsiyar da ya tsinanan mishi ba. Idan zasu hadu sai su taru su kone kwalayen kowa ma ya huta.

Ba a kasar Afirka ta Kudu kadai wadanda suka kammala karatun jami’a ke wannan korafin ba. Hatta a kasashe irin su Najeriya, masu kwalin digiri kan koka da irin yadda basu samun aiki matukar basu da ubangida ko wata hanya da za ta kai su wajen.

Wannan lamarin yayi kamari ta yadda za a ga masu digiri sama da goma a layi suna zaune babu abin yi. Hakan ke sa wasu tunanin cewa a da ne fa ilimi ya zama gishirin zaman duniya. Yanzu ba haka abun yake ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel