Yadda Tinubu Ya Kinkimi Mutane Fiye da 1400 Wajen Taron COP28 a Kasar Waje

Yadda Tinubu Ya Kinkimi Mutane Fiye da 1400 Wajen Taron COP28 a Kasar Waje

  • Najeriya ce kasa ta uku a yawan tawaga a taron COP28 da aka gudanar a kasar UAE a karshen makon nan
  • Baya ga kasar UAE mai karbar masaukin baki, Brazil ce kadai ta sha gaban Najeriya mai mutane 1400
  • Mutane sun soki yadda Bola Ahmed Tinubu ya dauki bataliya a sa’ilin da yake kukan rashin kudi a Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Dubai - A duk cikin kasashen Afrika da ke halartar taron COP28 da aka shirya a Dubai a kasar UAE, Najeriya ta fi kowa yawan tawaga.

Bayanan da aka samu daga hukumar UNFCCC ta majalisar dinkin duniya ya nuna Najeriya ta dauki mutum fiye da 1, 400 zuwa taron.

A duk Duniya, The Cable ta ce Najeriya ce ta uku – bayan kasar UAE inda ake taron sai kuma Brazil masu mutum 4,409 da 3,081.

Kara karanta wannan

Jerin manyan yan siyasar Najeriya 10 da aka haifa a watar Disamba

Bola Tinubu
Bola Tinubu a taron COP28 a Dubai Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya je Dubai da mutane 1411

Najeriya da Sin sun tafi taron sauyin yanayin dauke da mutane 1, 411 a tawagarsu duk da irin yadda Dalar Amurka ta tashi a kan Naira.

Wannan taro da Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin kasashen duniya su ka halartar ya samu halatar mutum fiye da 84, 100.

Kamar yadda Carbon Brief ta fitar da rahoto ranar Juma’a, adadin masu halartar ya zarce wadanda su ka je taron COP27 a kasar Masar.

A tsawon shekaru 30, ba a taba samun taron da ya cika kamar na wannan karo ba.

Ministoci da taurari sun tafi COP28

Legit ta duba jerin ‘yan Najeriya da ke wajen taron, ta lura fiye da rabin Ministocin Najeriya su na kasar tarayyar Larabawan a yanzu.

Baya ga jami’an gwamnati, jaridar ta ce kungiyoyi masu zaman kan su da taurari su na cikin wadanda aka yi wa rajistar zuwa taron nan.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun halaka dan bindiga, sun ceto malamin addini da wasu mutum 2 a jihar arewa

Jama’a suna ganin tawagar Najeriya ta yi yawa musamman ganin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke ta kokawa kan rashin kudi.

Baya ga kudin jirgi, gwamnati za ta kashe kudi a otel da kudin sallama na DTA da za a biya, wasu na ganin hakan zai sa Dala ta kara tashi.

Kasafin kudin Tinubu ya jawo surutu

Ana da labari Hon. Yusuf Shitu Galambi ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kawo kundin kasafin kudi wayam babu bayanan kudin da za a batar.

‘Dan majalisar ya ce a tarihin majalisa ba su taba ganin an kawo akwatin kasafi babu komai a ciki ba, zancen da ya jawo aka yi masa raddi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng