Gobara ta Kama a Babbar Jami’ar Arewacin Najeriya, ABU Zaria a Ranar Juma’a

Gobara ta Kama a Babbar Jami’ar Arewacin Najeriya, ABU Zaria a Ranar Juma’a

  • Babban ginin da ke dauke da ofisoshin shugabanni da ma’aikatan jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya gamu da gobara
  • Wuta ta kama ne a jami’ar a ranar Juma’ar nan, amma wani jawabi da ABU Zaria fitar ya nuna gobarar ta zo da sauki
  • Shugaban jami’ar, Farfesa Kabir Bala ya ziyarci inda abin ya faru bayan masu kashe gobara sun shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ginin da ke dauke da ofishin shugabanni da ma’aikatan jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya kama da wuta a ranar Juma’a.

A yammacin ranar 1 ga watan Disamba 2023, wuta ta kama ci a katafaren ginin mai hawa takwas kamar yadda Legit ta samu labari.

Kara karanta wannan

Alkalan da suka yi kuskure a shari’ar zaben Kano za su yabawa aya zaki a Majalisar Shari’a

ABU Zaria
Gobara ta kama a ABU Zaria Hoto:www.abu.edu.ng
Asali: UGC

Daga baya jawabi ya fito daga sashen hulda da jama’a na jami’ar, aka yi bayanin yadda wutar ta barke da duk matakan da aka dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ABU Zariya ta fitar da jawabi

Shugaban sashen hulda da jama’a na ABU Zariya, Malam Auwal Umar ya ce gobarar ta fara ci ne da kimanin karfe 4:15 na yammacin jiya.

A jawabin, jami’ar ta ce ba a iya gano abin da ya jawo gobarar zuwa yanzu ba tukuna, amma an kafa wani kwamiti domin ya yi bincike.

"Babu rauni ko wani hadari da aka samu. Sai dai na’urar raba wutar lantarki da wasu na’urorin sauti da aka manta da su sun kone

Matakin gaggawan da jami’an kwana-kwana da na tsaro su ka dauka ya taimaka. Asali ma dai tuni har an maida wuta a ofisoshin."

- ABU Zariya

Kara karanta wannan

Ana shirye shiryen gyara a PDP, za a kira taron zaben shugabanni 3 a Majalisar NWC

Shugaban ABU Zariya ya ziyarci wurin

Tribune da ta kawo rahoton jawabin, ta ce shugaban jami’ar watau Farfesa Kabir Bala da wasu shugabanni sun ziyarci wurin nan take.

Farfesa Kabir Bala ya yi Allah ya kyauta, ya kuma yabawa kokarin ma’aikatan jami’ar.

Dalibin ABU Zariya ya ce abin da sauki

Wani dalibi da ke karatun difloma ya shaida mana cewa wutar ta shafi hawan farko ne na ginin amma ya ce gobarar ta zo da sauki sosai.

An ga masu gadi da motar kashe gobara sun yi gaggawar isa da jin abin da ya faru.

Hakan ya faru kenan awanni bayan Sheikh Abubakar Sa’ad ya jagoranci sallar juma’a yayin da mafi yawan dalibai su ke gida a halin yanzu.

Rasuwar tsohon shugaban ABU Zariya

Kwanakin baya ne aka samu labari Allah Mai girma ya yi wa tsohon shugaban jami'ar ABU Zariya, Farfesa Abdullahi Mahadi, rasuwa.

Kara karanta wannan

Matakin da Gwamnatin Tinubu ta dauka ya jefa karatun Amaechi da Melaye a hadari

Marigayin, wanda shi ne shugaban farko na jami'ar jihar Gombe, ya rasu ne a daren Jumu'a, 16 ga watan Disamban 2022 yana da shekaru 77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng