Yadda wasu ‘Yan Baiwa 3 daga Bauchi suka zo birnin ilmi, suka bar tarihi a ABU Zaria

Yadda wasu ‘Yan Baiwa 3 daga Bauchi suka zo birnin ilmi, suka bar tarihi a ABU Zaria

  • Sai da aka shafe shekaru 20 ba a samu mai digirin 1st class a fannin ilmin jinya (BNSc) a ABU Zaria ba
  • A shekarar 2017 ne aka samu wani hazikin dalibin, Usman Usman Muhammad da ya ciri tuta a jami'ar
  • Bayansa an samu wasu dalibai biyu da suka zo daga jihar da ya fito ta Bauchi, da suka bi sahunsa

Kaduna - Tun da aka kafa sashen ilmin jinya a jami’ar Ahmadu Bello watau ABU Zaria, mutane uku kacal aka iya samu suka fita da mafi kyawun digiri.

Abin ban mamaki da sha’awa, duka wadannan hazikan dalibai uku sun fito ne daga jiha guda - Bauchi. Jaridar The Nation ce ta fitar da wannan rahoto.

A shekarar 2017, Usman Usman Muhammad ya yi abin da ba a taba samun wanda ya yi ba tun shekarar 1997 da aka fara karantar da fannin jinya a ABU.

Kara karanta wannan

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

Usman Usman Muhammad ya kammala karatun digirin BNSc a jami’ar da makin CGPA 4.50. Hakan ya zaburar da wasu ‘yan bayansa ‘yan jihar Bauchi.

Wasu sun bi sahun 'dan garinsu

Bayan Usman an samu wani takwaransa, Usman Muhammad da kuma Abdullahi Muhammad Bello da suka samu shafi a wannan sabon littafi da ya bude.

ABU Zaria
Jami'ar ABU Zaria Hoto: Kabiru Danladi Lawanti / @elkabir
Asali: UGC

Yayin da Usman Muhammad ya fita da maki 4.66 (wanda ya zarce na kowa a tarihin sashen), Abdullahi Muhammad Bello ya bar tarihi ne da maki 4.55.

Su biyun sun fito ne daga karamar hukumar Kirfi, shi kuma Usman Usman Muhammad wanda ya fara share masu hanya mutumin karamar hukumar Bauchi ne.

Sun samu horo a gida

Wannan rahoto ya ce wani abin ban sha’awa shi ne dukkaninsu ukun sun yi karatu a makarantar koyon ilmin aikin jinya a garin Bauchi kafin zuwansu jami’ar.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Duk da Muhammad ya fara wannan makaranta, bai kare ba sai da ya samu gurbin ajin farko a jami’ar ABU Zaria da jarrabawarsa ta UTME, sai ya baro Bauchi.

Shi kuma takwaran na sa ya ce ya tsaya har ya samu difloma a makarantar, sannan ya shigo aji biyu a jami’a, a nan ya ci karo da mutumin garin na su a 500L.

Bello yana gaban Muhammad a School of Nursing. Sirrrin dukkansu dai kusan shi ne sun zo da shirinsu da kuma maida hankali ganin sasshen na su ya yi suna.

Bunkasa ilmi a Yobe

Dazu ne aka ji Shugaban kamfanin Mangal Group, Dahiru Barau Mangal ya bada gudumuwar kudi Naira biliyan 1 ga jihar Yobe domin a bunkasa sha'anin ilmi.

Alhaji Dahiru Barau Mangal, Aliko Dangote da wasu manyan masu kudi sun bada wadannan kyaututtuka ne yayin da Mai Mala Buni ya mika kokon bara.

Kara karanta wannan

Wanda ICPC ta ke zargi da laifin satar Naira miliyan 900 yana so ayi sulhu a wajen kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel